1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari a gabashin Jamhuriyar Nijar ya hallaka mutane uku

Salissou BoukariAugust 28, 2015

'Yan Boko Haram, sun kai hari a garin Abadam da ke cikin jihar Diffa a gabashin Jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka mutane uku cikinsu har da wani sojan Nijar daya.

https://p.dw.com/p/1GNVg
Hoto: Reuters/J. Penney

Wannan harin ya wakana ne tun a farkon wannan mako amma kuma sai a yammacin jiya Alhamis aka samu labarin daga wata majiya ta jami'an tsaron kasar. A kalla dai 'yan gudun hijira dubu 150 ne da suka guje wa yakin da ake da Boko Haram daga Najeriya, ke a yankin Jihar Diffa, inda gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta saka dokar ta-baci, tare kuma da kame mutanen da ake zarki da alaka da 'yan kungiyar ta Boko Haram da yawansu ya kai mutune 1.100 kawo yanzu.