1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin ƙasa na ƙasar Indiya ya yi hatsari a gabacin ƙasar

May 28, 2010

Mutane 65 suka mutu a sakamakon hatsarin jirgin ƙasar da ya auku a ƙasar Indiya

https://p.dw.com/p/Nb9H
Wani jirgin ƙasa na ƙasar IndiyaHoto: AP

Wani abu da ya fashe a gabacin ƙasar Indiya, ya yi sanadiyar kaucewar wani jirgin  ƙasa daga kan hanyarsa. Jirgin wanda ya taso daga Bombai zuwa Cal-culta ya kuma ci karo da wani jirgin ƙasar da ke ɗauke da kayayakin yan kasuwa.

Mutane a ƙalla guda  65 suka mutu a sakamakon wannan hatsari da ake kyautata zaton cewa ƙungiyar yan tawayye na Maoiste sune umul-haba'isin aukuwar haɗarin.

Gidan Talabijin na ƙasar ya nuno hotunan tarkacen jirgin da ya yi kaca kaca, wanda kuma wasu da dama daga cikin fasinjojin suke sarƙe cikin tarkacen ,  

Ministan sufurin jiragen ƙasa na Indiya Mamata Banerjee, wanda ya tabbatar da cewa yan tawaye sune suka ɗana bam ɗin, ya shedda cewa a kwai yiwuwar samun ƙaruwar adadin mutane da hatsarin ya rutsa da su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.

Edita        : Abdullahi    Tanko  Bala.