1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani matashin Ruwanda ya zama abin misali na kasuwanci

Johannsen, Jesko/MNASeptember 2, 2015

A kasar Ruwanda wani matashi dan kasuwar kasar, Serge Ndekwe da tun yana da shekaru 18 ya fara tuki a matsayin direban tasi yanzu ya zama abun koyi.

https://p.dw.com/p/1GQ21
DW Sendung Africa on the Move
Hoto: DW

A kasar Ruwanda wani matashi dan kasuwar kasar, Serge Ndekwe da tun yana da shekaru 18 ya fara tuki a matsayin direban tasi, kana daga bisani ya koma direaban babbar mota. Yanzu haka dai ya bude wani gidan abinci da kuma masana'antar sarrafa madara, bayan ya sha fadi tashi cikin kananan harkokin kasuwanci.

Joghurt Fabrikation von Serge Ndekwe
Hoto: DW

Ana ci gaba da aiki a wani abin da ke zama gagarumin aiki na farko da Serge Ndekwe ya bude. Shi dai wannan matashi dan kasuwa na Ruwanda ya zuba jarin dubban Euro cikin wani gidan abinci na Italiya, da ke zama babban aikinsa na farko. Dan shekaru 35 ya yi bayani yadda mahukunta suka rufe gidan abincin jim kadan bayan bude shi saboda hayaniya. Ya kashe kudi da yawa da ya kusan durkusar da shi.

DW Africa on the move - Serge Ndekwe
Hoto: DW

Serge Ndekwe na da kuma masana'antar sarrafa madara da ya fara ginawa shekaru takwas da suka wuce. Kamar gidan abincin, sau biyu ana rufe masana'antar saboda dalilai na rashin tsabta. Akwai jita-jitar cewa kamfaninsa barazana ce ga kamfanonin sarrafa madara na gwamnati. Yanzu ana samun kayayyakin Ndekwe a kowane shago cikin Ruwanda.

Dan kasuwar na shirin fadadawa da zamanantar da aikinsa.

Mutane 12 ke yi masa aiki yanzu. Amma ya na son ninka yawansu. Domin ita ce hanya daya da zai iya cika ka'idojin sarrafa madarar.

A kullum masana'antar na sarrafa madara fiye da lita 1000. Suna kuma sarrafa kindirmo da cuku. Yanzu haka dai wannan dan kasuwa na shirin gina wurin shakatawa a wajen birnin Kigali, duk da matsaloli da yake fuskanta jefi-jefi.

Wannan dai shi ne abin da wannan dan kasuwar ke yi. Yana samar da guraben aiki ga 'yan uwansa 'yan kasa yana kuma bai wa Ruwanda siffa ta zamani.