1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Leipzig tana kan gaba a wasannin Bundesliga

Gazali Abdou Tasawa AH
September 2, 2019

Leipzig ta karbe ragamar Bundesliga bayan da ta kasance kungiyar da ta ci wasanninta uku tun bayan soma wasannin na bana. Yayin da a Maroko Aka kammala wasannin tsalle-tsalle da guje-guje nja Afirka karo na 12.

https://p.dw.com/p/3Osmk
Fußball Bundesliga | Eintracht Frankfurt vs. Fortuna Duesseldorf
Hoto: Bongarts/Getty Images/A. Grimm

 A wasannin Bundesliga na Jamus ta canza zane a saman tebirin na Bundesliga wanda kungiyar Leipzig ta dare da maki tara bayan a ranar Juma'a ta bi Mönchengladbach har gida ta kuma lallasata da 3-1, yayin da Bayern Münich ta taso daga matsayi na shida zuwa na biyu da maki bakwai, bayan da ta karbi bakuncin Mainz ta kuma wulakantata da ci 6-1,  a yayin da Wolfsburg ke a matsayi na uku da maki bakwai. Dortmund wacce ta yi raggon kaya a lokacin da ta je bakunci a birnin Berlin inda ta sha kashi da ci 3-1 a gaban Union Berlin ta sauka daga tebirin na Bundesliga zuwa matsayi na biyar da maki shida.