1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'abota kwallon kwando na jimamin rasuwar Kobe Bryant

Suleiman Babayo MNA
January 28, 2020

Alhinin da ake nunawa sakamakon mutuwar daya daga cikin shahararrun 'yan wasan kwallon kwando na Amirka sai lig na Jamus da ake kira Bundesliga da wasu wasanni.

https://p.dw.com/p/3WsC2
USA Kobe Bryant Gedenkstätte am Staples Center in Los Angeles
Hoto: picture-alliance/ZumaPress/R. Chiu

Ana ci gaba da nuna alhini daga bangarori dabam-dabam na duniya sakamakon mutuwar shahararren dan wasan kwallon kwando na Amirka mai suna Kobe Bryant wanda ya bar duniya sakamakon hadarin jirgin sama mai saukar ungulu tare da 'yarsa 'yar shekaru 13 da haihuwa gami da wasu mutane bakwai da ke cikin wannan jirgi.

Kobe Bryant wanda ya bar duniya yana da shekaru 41 da haihuwa ya kasance daya daga cikin fitattaun 'yan wasan kwallon kwando da suka taka dogon kasa kuma ya samu kyaututtuka dabam-dabam da ake samu a wannan wasan na kwallon kwando mai tasiri a kasar Amirka.

Bundesliga

A wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga kuwa, yayin wasannin da aka kara Borussia Dortmund ta doke FC Kolon 5 da 1, kana Union Berlin ta doke Augsburg 2 da nema, a nata bangaren Paderborn ta bi Freiburg ta lallasa ta 2 da nema, ita kuwa Hertha Berlin ta doke Wolfsburg 2 da 1, sannan Bayern Munich ta yi cin kacar tsohon keke rakacau ga kungiyar kwallon kafa ta Schalke 05 da nema, ita ma Leverkusen ta doke Düsseldorf 3 da nema. A wasan da muka kawo muku kai tsaye daga nan Sashen Hausa na DW, a ranar Asabar kungiyar Frankfurt ta doke Leipzig 2 da nema.

Fussball 1. Bundesliga 19.Spieltag l Eintracht Frankfurt v RB Leipzig l Enttäuschung Timo Werner
Timo Wagner na kungiyar Leipzig. Duk da kashin da ta sha a hannun Frankfurt har yanzu Leipzig din ce ke a saman teburin BundesligaHoto: Imago Images/Eibner Pressefoto/Weiss

Ya zuwa yanzu Leipzig ke jagorancin teburin na Bundesliga a Jamus da maki 40 inda ta wuce kungiyar Bayern Munich da maki daya, wadda take da 39, a matsayi na uku akwai kungiyar Mönchengladbach mai maki 38, yayin da a mastayi na hudu kungiyar Borussia Dortmund take da maki 36, a matsayi na biyar akwai kungiyar Leverkusen mai maki 34.

Wasannin La Liga a kasar Spain

A wasan lig na La Liga da aka kara a kasar Spain, kungiyar Real Madrid ta bi kungiyar Real Valladolid har gida ta doke ta ci 1 mai ban haushi, yayin da ita kuma Valencia ta doke Barcelona 2 da nema.

Ita dai kungiyar Real Madrid ke rike da teburin da maki 46, Barcelona tana matsayi na biyu da maki 43, ita kuwa Sevilla mai maki 38 tana matsayi na uku, a matsayi na hudu akwai kungiyar Getafe mai maki 36, a matsayi na biyar akwai kungiyar Atletico Madrid mai maki ita ma 36.

Wasannin zakarun kungiyoyin Afirka

A wasan cin kofin zakarun nahiyar Afirka kungiyar kwallon kafa ta Zesco United da ke Zambiya ta tashi 1 da 1 da kungiyar Primeiro Agosto ta Angola, sannan Zamalek ta Masar ta tashi babu wanda ya jefa kwallo a raga da kungiyar Mazembe ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Kasar Masar ta lashe kambun gasar kwallon hannu ta nahiyar Afirka da aka gama ranar Lahadi a birnin Tunus na kasar Tunusiya, a karawar da ta yi da takwararta mai masaukin baki a gasar, wato kasar Tunusiya.