1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyaututtuka da ake ba wa 'yan kwallon kafa

Gazali Abdou Tasawa MNA
September 30, 2019

Wasannin Bundesliga na karshen mako bai yi wa kusan illahirin kungiyoyin da suka karbi wasa dadi ba, domin kuwa daga cikin wasanni tara, takwas an lallasa kungiyar da ta karbi bakuncinsa.

https://p.dw.com/p/3QVF8
1. Bundesliga | FC Bayern München - 1.FC Köln | Coutinho
Hoto: picture-alliance/Laci Perenyi

A cikin shirin za ku ji cewa Yaya Babba Bayern Munich ta karbe tebirin gasar Bundesliga. Za mu leka a birnin Doha domin jin inda aka kwana a gasar wasannin guje-guje ta duniya. Shin kun san babbanci da ke da akwai tsakanin kyaututuka biyu na The Best Fifa da kuma Ballon d'or da ake bai wa dan wasan kwallon kafa mafi bajinta a duniya a kowace shekara.

Bari mu yaye labulan shirin namu da gasar Bundesligar kasar Jamus inda a karshen mako aka buga wasannin mako na shida. Sai dai wani abun da ya dau hankali a wasannin na wannan mako shi ne yadda wasan bai yi wa kusan illahirin kungiyoyin da suka karbi wasa dadi ba, domin kuwa daga cikin wasanni tara da aka buga, takwas an lallasa kungiyar da ta karbi bakunci ne, inda Frankfurt ta ishe Union Berlin a gida ta doke ta da ci 2-1, Hoffenheim ta kwashi kashinta a hannu a gida da ci 3-0 a gaban Mönchengladbach, Wolfsburg ta bi Mainz a gaban magoya bayanta ta doke ta da ci daya mai ban haushi, Leverkuzen ta je bakunci a Augsburg ta kuma fi ta iya rawa da ci 3-0, kazalika Freibug ta bi Düsseldorf a gida ta doke ta da ci daya mai ban haushi, Leipzig wacce ba ta baras da wasa ko daya ba tun bayan soma a wasanni na bana da kuma ke a kan tebirin na Bundesliga tun surmiyo kasa bayan da Shalke 04 ta iske ta a gidanta ta ko daka mata dan karan kashi da ci 3-1. Haka lamarin ya kasance ga makobtanmu na birnin Kolon wadanda Hertha Berlin ta wulakanta a gida da ci 4-0, a yayin da da kyar da jibin goshi Yaya Babba Bayern Münich ta sha daga hannun Paderbon da ci 3-2.

Borussia Dortmund ita kadai ce daga cikin kungiyoyin da suka karbi bakunci da ba ta sha kashi ba, amma ita ma da kyar da jibin goshi ta tashi ba kare bin damo tsakaninta da Bremen inda suka tashi ci 2-2.

A jimulce dai kwallaye 21 aka zura wa kungiyoyin da suka karbi bakunci a wasannin makon na shida a Bundesliga a yayin da su kuma suka zura shida kadai. A yanzu dai mai abu ya karbi abinsa inda Yaya Babba Bayern Münich ta karbe tebirin na Bundesliga da maki 14, Leipzig na bi mata da maki 13, Freiburg na a matsayin ta uku da maki 13 ita ma. A yayin da aka jefar da yaya karama Dortmund a matsayin takwas da maki 11.

Kyaututtukan The Best FIFA da kuma Ballon d'or

Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafan amma a wannan karo a kan batun kyaututukan da ake karrama dan wasa mafi bajinta a duniyar kwallon kafa a kowace shekara domin kuwa kwanakin kalilan bayan bayar da kyautar gwarzon dan kwallon duniya na FIFA ta shekara ta 2019 wacce Leonel Messi ya lashe, yanzu haka ma'abota kwallon kafa da dama ne ke cikin rudani na kasa tantance babbancin da ke da akwai tsakanin kwaitar FIFA The Berst da kuma ta Ballon d'Or wacce ake bayarwa a watan Disemban kowace shekara. Mouhamadou Awal Balarabe ya gudanar da bincike inda ya warware zare da abawa a wanann batu mai sarkakkiya, ga kuma rahoton da ya hada mana.

Na farko dai ita kwautar ballon d'or kwata ce da ainahi mujallar France Football ta kasar Faransa ta kirkiro a shekara ta 1956 da zimmar karrama dan wasan da ya fi kowa hazaka a wasannin Lig-lig na Turai kadai a shekara a shekara. kuma dan wasan kasar Kuroshiya da ke buga wa kungiyar Real Madrid wato Luka Modric shi ne ya lashe kyautar ta shekarar da ta gabata ta 2018 da ke zama a matsayin ta 63 tun bayan soma bayar da ita.

Lionel Messi da Megan Rapinoe su suka ci kyauta mafi girma ta FIFA Best a 2019
Lionel Messi da Megan Rapinoe su suka ci kyauta mafi girma ta FIFA Best a 2019Hoto: picture-alliance/Zumapress/J. Moscrop

Sai a shekara ta 1991 ne ita hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta kirkire wannan kyauta tata ta Fifa The Best  ko gwarzon Fifa wacce take bai wa dan wasan da ya fi bajinta a shekara a wasannin lig-lig na duniya baki daya, sabanin ballon d'or da ke shafar wasannin lig-lig na Turai kadai. Kuma Luka Modric wanda ya lashe kyautar Ballon d'or na 2018 shi ne kuma ya lashe kwatar ta gwarzon dan wasan FIFA wannan shekara. Leonel Messi ya lashe ta wannan shekara ta 2019.

Sai dai a shekara ta 2010 hukumar FIFA da Mujallar France Football sun hade kyautukan nasu biyu na gwarzon dan wasan duniya a wuri daya a bisa sunan Ballon d'or FIFA.  To amma a shekara ta 2016 sabon shugaban Hukumar ta Fifa da aka zaba Gianini Infantino ya soke wannan tsari na kyauta daya tare da sake maido da kyautukan biyu na gwarzon Fifa da kuma Ballon d'or.

Wani bambancin na dabam da ke da akwai tsakanin kyaututukan biyu shi ne a fannin Ballon d'Or , kwararrun 'yan jarida a fannin labarin wasanni daga kasashe duniya dabam-dabam ne kadai ke kada kuri'ar zaben dan wasan na shekara, a yayin da a kyautar Gwarzon FIFA 'yan jarida da masu horas da kungiyoyin kwallon kafa da keptain Kepten na kungiyoyin kwallon kafa da kuma har ma da sauran 'yan kallo ne ke kada kuri'a a zaben.

Tun dai bayan da aka fara soma wadannan kyaututtuka biyu a dabam-dabam a kullum dan wasan da ya lashe kyautar gwarzon Fifa na shekara shi ne ke kuma samun ta Ballon d'Or ta shekarar, ban da amma a shekara ta 2004 inda Andry Chevchenko dan wasan kasar Ukraine ya lashe kyautar ballon d'Or a yayin da Ronaldiniyo na Brazil ya samu ta gwarzan Fifa ta wannan shekara. .

Sai dai shekaru 63 bayan assasa kyautar Ballon D'Or da  kuma shekaru 28 na  Gwarzon Fifa, har yanzu babu wani dan kwallo na wata liga da ba ta Turai ba da ya taba daukar daya daga cikin wadannan kyaututtuka biyu na zakarun kwallon kafa na duniya. Mista Gorge Weah shugaban kasar Laberiya na yanzu shi ne daya dayan dan Afirka da ya taba samun wannan kyauta ta Ballon d'Or  a shekara ta 1995 a lokacin yana murza wa kungiyar AC Milan leda. Lev Yachine mai tsaron raga na kungiyar Dinamo de Moskou shi ne daya dayan mai tsaron raga da ya taba lashe kyautar ta ballon d'Or a shekara ta 1963. 

Tun dai bayan da Kaka na kasar Brazil ya lashe kyautar a shekara ta 2007 to Leonel Messi da Christiano Ronaldo ba su sake barin wani ya lashe wadannan kyaututtuka ba inda kowannensu ya dauka so biyar. Amma a shekara ta 2018 ne Luka Modric dan Kuroshiya ya karya kambun nasu inda ya lashe kyautukan biyu. Sai dai kuma a wanann shekara ta 2019 Dan Aljana leonel Messi ya sake karbe kyautar gwarzon FIfa. Yanzu kuma duniyar kwallon kafa ta zura ido tana jiran ranar biyu ga watan Disamba mai zuwa domin sanin ko Messin zai kuma lashe kyautar ta Ballon d'Or ta bana ko kuma wani dan wasan zai same ta kamar yadda ta kasance a 2014 tsakanin Chevchenko da Ronaldiniyo na Brazil.

Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na 2019

Yanzu kuma sai gasar wasannin guje-guje ta duniya da ke gudana a Doha babban birnin Katar.

Leichtathletik-WM 2019 100 Meter  Siegerin Shelly-Ann Fraser-Pryce
Shelly-Ann Fraser-Pryce bayan ta lashe tseren mita 100 a DohaHoto: AFP/J. Samad

A ranar Lahadi 'yar kasar Jamaika Shelly-Ann Fraser-Pryce ta lashe gasar tseren mita 100 a cikin sakon 10 da dakikoki 71. Wannan shi ne karo na hudu da 'yar gudun kafan mai tsawon mita daya da centimeta 60 kacal ke zama zakarar duniya baya ga zakarar wasannin Olympic so biy a fannin tseren na mita dari.

Kasar Amirka ta lashe gasar gudun yada kanen wani ta mita 100 sau hudu ta gaurayen maza da mata a cikin mintuna uku da sakon 9 da dakika 34, a yayin da kasar Chaina ta lashe wasan tseren tafiyar kilomita 20 na mata a cikin awa daya da mintoci 32 da kuma dakikoki 53.

Idan mun dawo a nan Jamus a jiya Lahadi Kenenisa Bekele dan kasar Ethiopiya ya lashe gasar gudun kafa mai zurfi ta Marathon ta birnin Berlin. Dan gudun kafan mai shekaru 37 ya lashe tseren na kilomita 42 da mitoci 195 a cikin awoyi biyu da minti daya da sakon 41. A bangaren mata ma Ashete Bekere 'yar kasar habashar ce ta lashe gasar a cikin awoyi biyu da mintuna 20 da sakon 14.