1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin kwallon kwando na Afrobasket

March 29, 2017

Birnin Brazaville na Kongo ne zai dauki bakwanci daga 13 zuwa 30 ga watan agusta na wannan shekara ta 2017.

https://p.dw.com/p/2aDyF
Sport Freizeit Basketball Basketballkorb
Hoto: Fotolia/Marcito

Kungiyoyin kwallon kwando na kasashen Afirka sun gudanar da wasannin neman cancantar shiga lig din wannan nahiya da aka fi sani da suna Afrobasket.

Kungiyoyi 10 ne dai suka samu tabbacin shiga gasar ciki har da na Tunisiya da Moroko a yankin Maghrib. Sai Senegal da Cote d'Ivoire da kuma Mali da ta doke Guinea a yankin yammacin Afirka. Yayin da a tsakiya da kuma gabashi da kudancin nahiyar afirka kuwa har yanzu ba a san maci tuwo ba, sai bayan an karawar karshe tsakanin Chadi da kamaru a cikin wannan mako, sannan an yi wasanni hudu da suka rage a gabashin Afirka.

Dama dai kwango Brazaville da ke shirya Afrobasket da kuma Tarayyar Najeriya da ke rike da kofin ba su bukatar karawa domin cancanta. Su ma Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da Yuganda da Masar suma sun samu gurbi tun da jimawa.