1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu kasashe sun yi alkawarin ba da sojoji da za´a girke a Darfur

September 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuiI

MDD ta ce ta samu alkawuran farko na ba da karo karon dakarun kiyaye zaman lafiya da ta ke shirin aikewa zuwa lardin Darfur na kasar Sudan. A wani taro na kasashe 50 da ke da niyar ba da gudunmawar sojoji da ya gudana a birnin New York, kasashen Norway, Tanzania, Nijeriya da kuma Bangladesh sun kasance kasashen farko da suka alkawarta ba da sojojin su. Wani kuduri da kwamitin sulhun MDD ya zartas kwanan nan ya tanadi samar da rundunar samar da zama lafiya mai sojoji dubu 20 wadda zata maye gurbin rundunar kungiyar tarayyar Afirka a Dafur. Har yanzu dai gwamnatin Sudan na adawa da girke sojojin na MDD a wannan yanki da yaki ya daidaita.