1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata Gobara ta hallaka mutane da dama a Ghana

Salissou BoukariJune 4, 2015

Fiye da mutane 70 ne suka rasu sakamakon gobara da ta tashi a wani gidan mai da ke Accra babban birnin kasar Ghana a yammacin jiya Laraba (03.05 2015).

https://p.dw.com/p/1Fblr
Ghana Tankstellenexplosion in Accra
Hoto: Reuters/M. Mpoke Bigg

Gobarar ta tashi yayin da mutanen ke neman wurin labewa a wannan gidan mai sakamakon wani ruwan sama mai karfi da aka yi wanda ya haddasa ambaliya a cewar jami'an tsaro na 'yan sanda da kuma masu aikin ceto na Red Cross. Gobarar dai ta wakana ne kusa da Shatale-tale na Kwame Nkrumah da ke tsakiyar birnin na Accra, kuma an zaton wutar ta tashi ne daga cikin wani gida da ke kusan gidan man.

Da ya kai ziyara wurin da hadarin ya faru cike da tausayi, Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama wannan rishi da aka yi wata babbar annoba ce ga al'ummar kasar ta Ghana, inda ya ce ya rasa ma kalmar da zai yi amfani da ita a wannan lokaci, yayin da manyan asibitocin birnin suka sanar cewa adadin da aka bayar na iya karuwa a nan gaba.