1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kotu a Nijar sa saki yan jaridun da aka kama

January 30, 2014

A wannan Alhamis ce wata kotu a birnin Yamai ta sallami wasu yan jaridu biyu da wani dan kungiyar farar hulla guda da hukumomin kasar suka tsare tun ranar Litinin da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1AzoP
Hoto: DWM. Kanta

Da yake bayani gaban 'yan jaridu, daga cikin 'yan jaridar da aka saki a wannan Alhamis, na cewa yanzu ne babban alkali ya sallamo ni. Ana tuhumata ne da laifin kage ga shugaban kasar, domin cikin mahawarar nace shugaban kasa yayi wa wata mata ta jihar shi alkawalin gina mata rijiya, shi ne aka tambayeni da na kawo hujja.

Shi ma daga nashi bangare gidan telebijin na Canal 3 dake birnin na Yamai ya tabbatar da sakin ma'aikacin nashi guda da aka kame mai suna Zakari Adamu.

Dan kungiyar farar hullar mai suna Nayussa Jimrau, cewa yayi lale babban Alkali ya sakemu domin ya ce a halin yanzu bai ga wani abu kwakkwara da zai sa ya ci gaba da rikemu ba.

An kama yan jaridar ne, bayan da suka halarci wata mahawara da aka yi a wani gidan telebijin mai zaman kanshi.

Kafin wadannan dai dama an kama wasu yan jaridun guda biyu kafin daga bisani a sakesu.

Tuni dai aka fara nunin kasar ta Nijar a matsayin wadda ta samu koma baya kan batun 'yancin fadar albarkacin baki a cewar hadin gwiwar kungiyar 'yan jaridu na Afirka dake da cibiya a birnin Dakar.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal