1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata sabuwar ƙungiyar kishin islama ta ɓullo a Najeriya

Sadissou YahouzaNovember 27, 2012

A yayin da ake sa ran warware rikice- rikicen da ke da nasaba da ƙugiyar Boko Haram,wasu mutane su yi iƙirarin kafa wata ƙungiya makamanciyar ta.

https://p.dw.com/p/16qcU
Harin da wata sabuwar kungiya ta kaiHoto: dapd

A wata sanarwa da ta rabawa manema labarai Kungiyar Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladi Sudan wanda shugabanta da bayyana da Abu Usamatul Ansar ya rattabawa hannu tace itace ke da alhakin wannan harin da aka kai a wata coci saboda ceto wadanda aka tsare kuma take zargin ana zalunta a irin wadan nan wurare.
Sanarwar wace ta kara da cewa kungiyar zata ci gaba da gudanar da irin wannan hare-hare matukar ba'a saki Musulmai da hukumomin suka kama a sassan arewacin Najeriya da sunan ‘yan ta'adda ne ba.
Wannan dai shine karo na farko da wannan kungiyar mai da'awar gwagwarmayar kafa shari'ar musulunci a daukacin nahiyar Afirka da dauki alhakin kai hari a tarayyar Najeriya mai fama da matsalar tabarbarewar tsaro sanadiyyar rikici-rikice da ake dangantawa addini da kuma kabilanci.
‘Yan Najeriya dai sun bayyana damuwa dangane da wannan labari saboda fargabat kara tabarbarewar lamuran tsaro a kasar inda suka zargi gwamnatin tarayyar kasar da kasa magance matsalar rashin tsaron duk da makudan kudaden da ake salwatarwa da sunan magance matsalar tsaro.
Ga ra'ayoyin wasu ‘yan Najeriya da suka bayyana fargabar dangane da aikin da wannan sabuwar kungiya ta bayyana alhakin dauka.
Ko wace matsalar bullar wannan kungiya zai iya haifarwa a dai-dai lokacin da ake kokarin magance matsalar tsaro da ta yi sanadiyyar rayuwa da dukiyoyin na miliyoyin Nairori.
Malam hamza Umar Usman wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a tarayyar Najeriya.
Ganin kowa na bayyana cewa yin adalci shine zai kawo karshe wannan matsaloli ya sa a baya na tambaya gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassa Dankwambo kan abinda su shugabannin suka fahimta da adalci sai yace.
Har ya zuwa yanzu dai hukumomin basu ce komai kan wannan ikirari da wannan sabuwar kungiyar gwagwarmaya tayi ba inda a bangare daya kungiyar ta nemi hadin kan al'umma don cimma nasarorin ta na tabbatar da adalco kamar dai yadda wannan sanarwa ta kunsa.

Bystanders gather around a burned car outside the Victory Baptist Church in Maiduguri, Nigeria, Saturday, Dec. 25, 2010. Authorities say dozens of assailants attacked the church on Christmas Eve, killing the pastor, two members of the choir and two people passing by the church. Police are blaming members of Boko Haram, a radical Muslim sect. (AP Photo - Njadvara Musa)
Hukumomi sun kasa shawo kan lamarin sai kaloHoto: AP
Nigeria Sicherheitskräfte Soldaten
An baza jami'an tsaro ko'inaHoto: Getty Images/AFP
Nigeria Kano Bombenanschlag
Hare-haren na ci-gaba da lakume rayukaHoto: Reuters

Mawallafa: Al-amin Suleman Mohamed/ Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi