1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Weah ya kama hanyar lashe zaben Laberiya

Ramatu Garba Baba
October 13, 2017

Sakamakon zaben kasar Laberiya na nuni da cewa tsohon gwarzon wasan kwallon kafa ta duniya George Weah na kan gaba wurin lashe zaben da ya gudana a wannan Talatar.

https://p.dw.com/p/2ll8h
Liberia Wahlen 2016 Anhänger DCC Partei
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

A sakamakon farko da hukumar zaben kasar ta bayyana na nuni da cewa Weah ke kan gaba bisa kuri'un da aka kiddaya na shiyoyi goma sha daya daga cikin goma sha biyar. Magoya bayan George Weah na cike da fatan shahararren dan kwallon zai cimma nasara na zama shugaban kasar ta Laberiya.

'Yan takarar ashirin ne suka fafata a wannan zaben don maye gurbin shugaba Ellen Johnson Sirleaf wacce ita ce mace ta farko da aka taba zaba a matsayin shugaba a Afirka. Ana sa ran hukumar zaben za ta fitar da sakamakon zaben baki daya a ranar 25 ga wannan watan na Oktoba kafin aje ga zagaye na biyu na zaben a watan Nuwamba mai zuwa in har aka gagara samun dan takarar da ya sami yawan kuri'u da rinjaye.