1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra´ila da Hezbollah

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buqm

Yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra´ila da ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Labanon.

A sahiyar yau, rundunar tsaron Isra´ila, ta yi lugudan wuta ga filin saukar jiragen samar Labanon, da ta ce, ta nan ne, ake jigillar makaman da Hezbollah ke anfani da su.

Kakakan rundunar Isra´ila, ya ce sun kai wannan hari, domin ladabtar da gwamnatin Labanon a kan halin ko in kulla, da ta ke nunawa, ga hare haren da Hezbollah ke wa Isra´ila.

Bugu da ƙari sojojin Isra´ila, sun kai ƙarin hare –hare, ta sararin samaniya, a kudancin Labanon, inda take, mutane kussan 30 su ka rasa rayuka.

Cemma, da yammacin jiya, dakarun Isra´ila, sun rugurguza wasu gadoji da ke haɗa kudu da arewancin Labonan.

Wannan hare hare na wakana, a matsayin martani ga kame sojoji 2 na Isra´ila, da yan ƙungiyar Hezbollah su ka yi.

Yan Hezbollah sun bayyana aikata hakan, domin nuna fushi, akan hare hare, babu ƙaƙƙabtawa da Isra´ila ke kaiwa Palestinawa.

Gwamnatin ƙasar Syria, ta hito hili ta yaba wa Hezbollah a kan hare- haren da ta abkawa Isra´ila.

Manazatra harakoki a gabas ta tsakiya, na masu hasashen, yankin baki ɗaya, ya tsunduma cikin wani yaƙin gama gari.