1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin neman zabe na Masar ya kankama

May 13, 2014

Yayin da ake shirin zaɓen shugaban ƙasar Masar cikin wannan wata na Mayu, ɗaya daga cikin abubuwan da suka fito fili shi ne cewa Abdul-Fattah al-Sisi zai lashe zaɓen.

https://p.dw.com/p/1Bz2P
Fattah al-Sisi
Hoto: Reuters

Yanzu haka hotunan tsohon babban habsan sojin ƙasar ta Masar Abdul-Fattah al-Sisi sun ratsa ko'ina cikin ƙasar, inda ake masa yaƙin neman zaɓe, sai dai kafin wannan lokaci shi ba wani mutumi ba ne fitacce. Ga abin da wani mai ƙaramin shago yake cewa:

"Ina son al Sisi, saboda unguwarmu ɗaya. Bayan haka kuma shi ne ya daƙile 'yan ta'adda da masu tsananin ra'ayi. Kuma da yardar Allah zai dawo ya ci gaba da ba da kariya."

A daya ɓangaren kuma Atef El Zaabalawi wanda suka yi yarinta tare da al-Sisi, kuma waɗanda suke masa yaƙin neman zaɓe tun daga tushe, ya ce ɗan takaran shugaban ƙasar mutum da ke da tarbiya ta gari:

Ägypten Präsidentschaftskandidat al-Sisi
Hoto: DW/M. Symank

"Lokacin da muke yara muna wasan ƙwallo a kan titi, kusa da gidansu Al Sisi, amma ba tare ba. Ya fito daga gidan kirki. Sun fi mayar da hankali kan karatu da aiki."

A matsayin babban habsan sojin Masar ya yi fice a fagen siyasar ƙasar lokacin da ya jagoranci kifar da gwamnati Shugaba Mohamed Mursi mai ra'ayin Islama na Ƙungiyar 'yan Uwa Musulmai, kuma tun lokaci ya shiga cikin fagen siyasar ƙasar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane