1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YADDA BATUN CIN HANCI DA RASHAWA KE ADDABAR KASAR KAMARU.

February 24, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlj
Rahotanni da suka iso mana daga kasar Kamaru sun shaidar da cewa a yanzu haka kasar na fama da matsalar cin hanci da rashawa a harkokin ilimin kasar,wanda hakan a cewar majiya mai karfi a kasar ka iya haifar da dan da bashi da ido a nan gaba kadan matukar dai ba,a shawo kann matsalar da wuri ba. Rahotannin sunci gaba da nunarwa cewa a yanzu haka akwai makarantu da dama a cikin kasar dake yin cucuwa cuwar sayar da takardar shaidar kammala karatun Diploma da ire iren makaman tansu.A hannu daya kuma da cuwa cuwar da wasu malaman keyi na kara kudin makaranta ba tare da sanin hukumar makarantar ba. A cewar babban sakataren harkokin ilimi na kungiyyar mabiya darikar Katolika na kasar mai suna Jean claude Ekobena, abin bai tsaya a nan ba kawai domin a wasu lokutan malaman na yin cuwa cuwar bawa dalibai maki na jarrabawa ba tare da gumin daliban ba,a wani lokaci ma har zana musu jararrabawar suke don karbar abin goro. Rahotanni dai sun tabbatar da cewa a shekara ta 1998 izuwa 1999 kungiyyar yaki da cin hanci da rashawa dake da cibiya a birnin Berlin na kasar Jamus ya shaidar da cewa kasar ta Kamaru itace ta karshe a jerin kasashe dake fama da wan nan matsala ta cin hanci da karbar rashawa. To amma kuma a shekarar data gabata a rahoton karshen shekara na kungiyyar ta Tranparency International ta dawo da kasar ta Kamaru a matsayi na 126 daga cikin kasashe 133 da akayi atisayen a kansu. A kuwa ta bakin wani malamin jamia dake kasar ta Kamaru mai suna Jacob Mekoul cewa yayi matsalar cin hanci da rashawa a bangaren ilimi a kasar abu ne dake yanayi da abin da yake faruwa a cikin alumma a fadin kasar ta Kamaru baki daya. Shi kuwa shugaban kungiyyar malaman makaranta na kasa Marianne Mebega cewa yayi babu shakka wan nan matsala ta karbar cin hanci da rashawa ta kai intaha a fannin ilimin a kasar ta Kamaru musanmamma bisa la,akari da koke koken da iyaye ke kawowa ofishin sa a kai akai. To amma duk da haka a cewar jamiin babu shakka kungiyyar sa na yin iya bakin kokarin ta wajen ganin abubuwa sun sai sai ta don inganta harkar ilimin a nan gaba. A wata sabuwa kuma bayan wan nan matsala da kasar ta tsinci kanta a ciki akwai kuma batun yadda masana ilimi na fannoni daban daban na kasar ke kaura daga kasar izuwa kasashen waje domin neman aiki mai tagomashi.Wanda hakan a cewar jamiyyún adawar kasar sakaci ne daga bangaren gwamnatin kasar na duba matsalolin malaman musanmamma don gujewar afkuwar hakan daga bangaren nasu. A kuwa kokarin da gwamnatin kasar keyi na kawo karshen wan nan mummunan aiki tuni gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai duba matsalar tare da bayar da shawara na hanyoyin da za,a bi domin kawo karshen matsalar a fadin kasar baki daya. Bugu da kari kwamitin kuwa a yanzu haka shine zai dinga kula da shigar dalibai makarantun sakandire na kasar sabanin shugabannin makarantun a hannu daya kuma da saye sayen kayan aiki a makarantun don amfani dasu wajen koyarwa ga daliban. A cewar shugaban kasar Paul Biya wan nan kwamiti daya kafa ya hada da gagga gangan tsoffin malaman makaranta na jamioi da masana na fannonin ilimi daban daban da kuma wakilai daga kungiyoyi masu zaman kansu.