1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar rigingimun a fagen siyasar Najeriya

Gazali Abdou Tasawa
June 7, 2018

A Najeriya a yayin da rikicin cikin gida na jam'iyyar APC mai mulki ke kara ta'azzara, wasu 'yan majalisar dokokin kasar sun yi yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga kan mulki.

https://p.dw.com/p/2z5Nk
Karikatur: Nigeria Politik Führung
Hoto: DW

Rigingimun siyasa na kara kamari a Najeriya inda rundunar 'yan sandar kasar ta gayyaci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, don ya amsa tambayoyi kan zargin kasancewa da hannu a mumunan fashi da makami da aka yi a garin Offa da ke jiharsa ta Kwara. Wannan batu ya haifar da rikicin cikin gida a jam'iyyar APC mai mulki inda 'ya'yan jam'iyyar PDP da suka yi majar shiga gwamnatin APC  suka kauracewa shirin neman sulhu. Ana cikin wannan ne kuma majalisar dokokin Najeriya ta yi barazanar tsige Shugaba Buhari idan bai cika wasu sharudda 12 da ta gindaya masa ba.