1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin yan jarida a kasar Cadi

Yahouza sadissouAugust 22, 2005

Hira da Martin Petry masharahanci akan al´ammuran yau da kullum a kasar Cadi.Ya bayana ra´ayi a game da yajin aikin yan jarida a kasar

https://p.dw.com/p/BvaK

Yau ne a kasar Cadi, kungiyoyin yan jarida, su ka shiga yajin aiki, domin nuna bacin rai, a kan yada Gwamnatin shugaba Idriss Debi, ke kuntatawa yan jarida, a ayyukan su, na yau da kullum, ta hanyar barazana, da yanke masu hukunce-hukunce dauri a kurkuku.

Wannan hali da yan jarida su ka tsinci kansu a ciki, da kuma sauran yanayin hakokin bani adama a kasat ya fara daukar hankullan kasashen dubia.

A game da haka na yi hira da Martin petry wani jami´in kungiyoyin bada taimakon raya kasa, da ke nan Jamus, wanda kuma ya share shekaru da dama a kasar Cadi.

A matsayin na masharahanci a kann al´ammuran da ke wakana a kasar na tambayi shi tunanin da yayi a game yajin aikin nay an jarida a kasar Cadi.

Malam Martin ya tabatar da cewa wannan yajin aiki ya zo daidai lokacin da yan jarida a kasar su ka shiga wani hali na ukuba da azaba daga gwamnati, tare da yanke masu hunkunci dauri iri -iri bayan an yi masu zargi na rashin adalci.

Mafi yawan tuhumar da gwamnati ke ma yan jarida a wannan kasa sun hada da buga labarin karya, da kuma tada fitina cikin kasa.

A dalili da wannan leffuka nen a baya bayan nan kotu ta yanke hukuncin daurin a kurkuku ga yan jarida hudu na kasar.

A wani abun mamaki kuma, yajin ya shafi yan jarida masu aiki a kafofin sadarwa na gwamnati.

A cewar Malam Martin, wannan ba abun mamaki ba ne,idan akayi la´akari ,da yadda suma yan jaridar gwamnatin, bayan shekaru da dama, suna matsayin yan amshin shata, su ka fara nuna alamomin samun yancin fadin albarkacin bakin su.

To saidai, duk da cigaban da su ka samu, ya zuwa yanzu, basu tsage gaskiya kamar yadda sauran abokan su ,na kafofin sadarwa masu zaman kansu ke aiwatarwa.

A bangaren hakokin bani adama, Malamin ya bayana cewa kasar Cadi na fuskantar matsaloli masu yawa.

Kungiyoyin kare hakokin jama´a ,na aiki bakin rai bakin fama, amma, har yanzu da sauran rina kaba.