Yaki da ayyukan ta'addanci a kasar Jamus
May 6, 2015Talla
A 'yan watannin baya-bayannan dai dama an yi ta kaiwa 'yan gudun hijirar hare-hare sai dai ba tare da an samu asarar rayuka ba. A yammacin ranar Talata ma dai an kona wani gida da aka tanada domin zaunar da 'yan gudun hijira a birnin Limburgerhof dake yammacin Jamus, yayin da irin haka ta faru a wani gidan na 'yan gudun hijira a farkon watan Afrilu a birnin Trögliz dake gabashin kasar. Mutanen dai da aka kama sun hada da maza uku da mace guda, kuma dukanninsu Jamusawa 'yan shekaru daga 22 zuwa 56 a cewar wata sanarwar da ofishin babban mai shigar da kara na gwamnatin ta Jamus ya fitar.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu