1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da ta'addanci a Aljeriya

January 17, 2013

Birtaniya ta ce za ta yi kawance da Aljeriya wajen warware rikicin sace jama'a.

https://p.dw.com/p/17Loi
Britain's Prime Minister David Cameron delivers his keynote speech at the Conservative Party conference in Birmingham, central England October 10, 2012. REUTERS/Toby Melville (BRITAIN - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Birtaniya ta ce ta yi amannar cewar hanyar da ta fi dacewa wajen kawo karshen matsalar sace mutane a kasar Aljeriya, ita ce yin aiki tare da gwamnatin kasar ta Aljeriya, maimakon yin gaban kai wajen tinkarar matsalar. Kakakin firayiministan Birtaniya David Cameron, ya fadi - a wannan Alhamis cewar, Mr Cameron ya cimma wannan matsayar ne bayan ganawar daya yi tare da firayiministocin kasashen Japan, da kuma Norway, wadanda 'yan kasashen su ke cikin jerin ma'aikatan kanfanin man fetur da wasu 'yan bindiga a kasar Aljeriya suka yi garkuwa da su.

A halin da ake ciki kuma ministan kula da harkokin wajen Birtaniya William Hague, ya ce ba za su yi gaggawar danganta garkuwa da wau 'yan kasashren waje a Aljeriya da rikicin kasar Mali ba:

Ya ce " Ina ganin za mu yi kaffa-kaffa wajen neman danganta garkuwa da 'yan kasashen mu da shiga tsakanin sojin da Faransa ta dauka a Mali. Ko da shike akwai yiwuwar bada wannan hsanzarin, amma yakan dauki lokaci gabannin tafka irin wannan ta'asar, maimakon danganta shi da batun tura soji zuwa Mali a makon jiya."

Tuni dai wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa dasu a Aljeriya suka tsere daga hannun wadanda suka tsare su.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu