1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zaben Amirka ya zafafa

November 5, 2012

'Yan takarancin shugabancin Amirka, Obama da Romney na gudanar da gangamin karshe na yakin neman zabe.

https://p.dw.com/p/16cmz
Hoto: AP

Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama da babban mai ƙalubalantarsa Mitt Romney na gangamin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe, yayin da wannan Talata Amirkawa ke yanke hukuncin wanda zai jagoranci ƙasar nan da shekaru huɗu masu zuwa.

Binkice na ƙarshe da aka gudanar na jan ra'ayin masu zaɓe ya nuna 'yan takara na mataki ɗaya na farin jini, abun da ke ƙara nuna rashin tabbas na wanda zai iya lashe zaɓen na Talata.

Yanzu haka 'yan takaran na ci gaba da gangami cikin jihohin da akasarin masu zaɓe basu yanke hukunci wanda za su zaɓa ba. Shugaba Obama na jam'iyyar Demokrat da Romney na jam'iyyar Republican na bin sahun ko wace kuri'a da ke ƙasar ta Amirka, domin tabbatar da samun nasara yayin zaɓen na wannan Talata.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Halima Balaraba Abbas