1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a zaben 'yan majalisa a Benin

Gazali Abdou Tasawa
April 25, 2019

Alamu na nuni da cewa zaben na wannan karo ba zai yi armashi ba a wasu yankunan kasar kamar Porto-Novo saboda yadda wasu yan kasar suka soma kosawa da koma bayan Dimukuradiyyar

https://p.dw.com/p/3HSTu
Benin Parlamentswahl | Wahlplakat
Hoto: DW/K. Gänsler

Duk da cewa yakin neman zaben na dab da kawo karshe harkokin siyasar sun kasance lami a birnin Porto-Novo idan aka kwatanta da lokutan yakin neman zaben a shekarun baya lamarin da ke da nasaba da yadda aka haramta wa jam'iyyun adawa da dama shiga zaben.

Wanann ce ta sanya jama'a cikin halin zaman dar-dar a wanann birni na Porto-Novo da ke zama cibiyar jam'iyyar adawa ta PRD inda mutane da dama suka nuna aniyar kaurace wa zaben 'yan majalisar da ke tafe. Bangarori daban-daban na kasar ta Benin sun sha alwashin haramta gudanar da zaben ta kowane hali.

Yanzu haka dai halin da ake ciki a kasar ta Benin ya soma tayar da hankalin kasashen duniya inda sai da ta kai Kungiyar Tarayyar Afirka aika tawaga zuwa kasar da zimmar samun cikakkun bayanai da kuma tattaunawa da bangarorin siyasar domin fahimtar kan yadda ake shirin gudanar da zaben.