1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawa a Mauritania sun ƙaurace wa zaɓen shugaban ƙasa

June 21, 2014

Ana kyautata zaton cewar shugaban mai ci Mohamed Ould Abdel Aziz shi ne zai sake samun nasara a zaɓen da 'yan adawar suka ce an shirya yin murɗiya.

https://p.dw.com/p/1CNZ8
Mauretanien Präsidentschaftswahl 2014
Hoto: Reuters

Shugaba Abdel Aziz wanda tsohon janar ne na soja mai shekaru 57 ya zo ne a kan karagar mulki a shekarun 2008 bayan wani juyin mulkin da ya yi. Kafin ya rikiɗe ya koma siyasa a kuma zaɓe shi a wani wa'adin mulki na shekaru biyar a shekarun 2009, a ƙarƙashin wani shirin na tattaunwa tare da shiga tsakanin ƙasashen duniya wanda tun a lokacin a zaɓen 'yan adawar suka yi ƙorafin cewar an tafka maguɗi.

Babu shakku Mohamed Ould Abdel Aziz shi ne zai samu nasara a zaɓen

Babu dai wani fargaba ana hasashen cewar shi ne zai samu nasara a zaɓen da ya gudana a jiya lami lafiya wanda sama da miliyan ɗaya da rabi na al'ummar ƙasar suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen. Ko da shi ke ma ana bayyana cewar umarnin da 'yan adawar suka bayar na a ƙaurace wa zaɓen ya sa jama'a ba su fito ba. jam'iyyun siyasar da ke adawa da shugaban waɗanda suka girga wata ƙungiya da ake kira da sunan FENDU na zarginsa da yin mulkin kama karya da kuma shirya yin murɗiya a zaɓen.

Präsident General Mohamed Ould Abdel Aziz
Hoto: AP

Mohammed Ould Abdel Aziz wanda shi ne shugaban Ƙungiyar haɗa kan Ƙasashen Afirka har ya zuwa shekarun 2015, na yin alfari da ƙaddamar da muhimman ayyuka a wa'adin mulkinsa na farko,ta hanyar yaƙar Ƙungiyar Al-Qaida, da kuma irin rawar da ya taka wajen kawo zaman lafiya a Mali da batun soke aikin bauta a ƙasar wanda aka tabbatar da ƙudirin a cikin kudin tsarin mulki tare da ƙaddamar da wani shirin tattaunwa da 'yan adawar. To amma wani mai yin sharhi a kan al'amura a ƙasar Mohammed Fall ya ce duk da haka wannan yunƙuri bai kawo ƙarshen rikicin siyasar ba a ƙasar.

''Ɓangare ɗaya na 'yan adawa ya yi watsi da wannan shiri tun daga lokacin shirin tattaunwar ya wargaje.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Lateefa Mustapha Ja'afar