1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa ba za su aminta da zaben Nijar ba

Salissou BoukariMarch 17, 2016

Gamayyar jam'iyyun adawa na COPA a Nijar ya yi kira da a kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta shirya zabuka masu iganci a kasar.

https://p.dw.com/p/1IFUr
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Alhaji Saini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD Nassara a NijarHoto: DW/M. Kanta

Gamayyar jam'iyyun adawa na COPA a Nijar masu goyon bayan takarar Malam Hama Amadou da a halin yanzu ya ke kwace a wani asibitin Amirkawa da ke kasar Faransa, sun ce ba za su amince da sakamakon zaben da za a yi na ranar Lahadi ba, inda suka yi kira da a kafa gwamnatin rikon kwarya wadda za ta shirya sabon zabe mai inganci a kasar.

Cikin wata sanarwa ce dai da ya fitar a wannan Alhamis din gamayyar 'yan adawan na COPA suka jaddada aniyarsu ta kin halartar zaben mai zuwa na ranar Lahadi, tare da yin kira ga magoya bayansu da su kaurace ma sa. Gamayyar 'yan adawan na Nijar dai sun soki wani abun da suka kira baba kere da manyan hukumomin da ke kula da zabe da suka hada da hukumar zaben kasar CENI da kuma Kotun tsarin mulkin kasar da gwamnati ke yi.

'Yan adawan na Nijar kuma sun yi kira ga 'yan kasar ta Nijar, da ma kasashen waje da su tashi tsaye na ganin an samu hawa kan teburin sasantawa tsakanin bangarorin kasar domin komawa ga cikeken tafarki na demokaradiyya.