1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na kalubalantar sakamakon wucin gadin zabe a Mozambik

Pinado Abdu WabaOctober 19, 2014

Sakamkon wucin gadin ya nuna cewa Simango ya sami kasa da kashi takwas cikin dari a yayinda Afonso Dhlakama ke da kashi 32 shi kuma Filipe Nyusi na Frelimo ke da kashi 62

https://p.dw.com/p/1DYUG
Hoto: DW/E. Saul

Jam'iyyar da ta zo na uku a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Mozambique ta sa kafa ta yi fatali da sakamakon zaben da aka gabatar kuma ta yi barazanar zuwa kotu.

Sakamakon wucin gadin da aka fitar na zaben da aka gudanar a wannan makon ya gwado shugaban jam'iyyar Mozambique Democratic Movement ko kuma (MDM) Daviz Simango a mataki na uku, bayan dan takarar jam'iyyar Frelimo mai mulki, Filipe Nyusi da kuma Afonso Dhlakama, madugun 'yan adawa daga jam'iyyar Renamo. Daya daga cikin manyan jami'an jam'iyyar ta MDM ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa cewa ba zasu amince da sakamakon ba ne saboda an hana wakilansu shiga runfunan zabe a lokacin da ake kada kuri'a abin da ya sabaawa tanadin dokokin zaben kasar.

Tuni dai hukumar zaben ta karyata zargin jam'iyyar MDM amma kuma shi kansa Dhlakama madugun 'yan adawa na jam'iyyar Renamo ya ce zaben bai yi tsabta ba kuma babu shakka zai kalubalanci gwamnatin Frelimo wanda dama ya yaka na tsawon shekaru 16 a yakin basasar da aka kammala a shekara ta 1992. Ana sa ran samun sakamakon karshe ran 30 ga wannan watan na Oktoba