1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na zanga-zanga a Banizuwela

Gazali Abdou Tasawa
April 26, 2017

'Yan adawa a Banizuwela sun sake kiran magoya bayansu domin gudanar da zanga-zanga da nufin tilasta wa gwamnatin Shugaba Nicolás Maduro shirya zabukan gamagari a kasar.

https://p.dw.com/p/2bvN8
Venezuela Proteste in Caracas
Hoto: Reuters/C. Veron

Wannan zanga-zanga dai ka iya zama mai cike da hadari kasancewa 'yan adawar na son yin tattaki ne har zuwa tsakiyar birnin Caracas wanda kezaman cibiyar jam'iyya mai mulki. A baya dai gwamnatin Shugaba Nicolás Maduro ta yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe duk wata zanga-zangar da aka shirya zuwa tsakiyar birnin na Caracas. Hukumomin shari'ar kasar ta Banizuwela dai sun tabbatar da mutuwar mutane 29 a yayin da wasu 437 kuma suka jikkata kana aka kame wasu mutanen 1.289 a yayin jerin zanga-zangar da 'yan adawar suka yi ta gudanarwa, tun daga farkon watan Afrilun da muke ciki da nufin nuna adawarsu da matakin kotun kolin kasar na karbe wani 'yanci na majalisar dokoki, wacce 'yan adawa ke da rinjaye a cikinta.