1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Siriya sun sauya alƙiblarsu

September 22, 2013

Bayan da suka ce ba za su kasance a tattaunawar sulhun da ƙasashen yamma suka shirya musu ba, sun sake tunani sun ce yanzu za su kasance amma kuma da sharaɗi.

https://p.dw.com/p/19m5e
Beschreibung: Ahmad Tumeh al-Chader: Regierungschef der syrischen Opposition. Datum: 14.09.2013 Rechte: Syrian National Coalition Angeliefert von Falah Elias am 14.9.2013
Ahmad Tumeh al-Chader shugaban majalisar 'yan adawaHoto: Syrian National Coalition

'Yan adawan Siriya sun yi amai sun lashe bayan da suka dawo suka ce zasu kasance a tattaunawar sulhun da kasashen Rasha da Amirka za su gudanar a ƙasar Switzerland, wanda daga farko suka ce sun janye. Manufar duk waɗanda za su kasance a wannan taron dai shine girka gwamnatin riƙon ƙwarya mai cikakken iko, a cewar shugaban majalisar 'yan adawan Siriyar Ahmad al-Chader, cikin wata wasiƙa da ya rubutawa Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Su dai 'yan tawayen na Siriya sun haƙiƙance kan cewa shugaban ƙasa Bashar al-Assad, ko ɗaya ba shi da wata rawar da zai taka a gwamnatin riƙon ƙwaryar da za a girka.

A na sa ɓangaren shugaba Bashar al Assad ba shi da niyyar barin madafun ikon ƙasar. Gwamnatin Jamus a nata waje kuma tana shirin ƙaddamar da wani sabon shirin diplomasiyya domin shawo kan wannan matsala na Siriya.

A cewar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, yanzu kowane ɓangare na sane da cewa matakin soji ba zai yi nasara wajen dakatar da yaƙin basasar ba. Kuma a dalilin haka ne a mako mai zuwa lokacin taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Jamus za ta matsa ƙaimi wajen ganin an tsagaita wuta a Siriya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal