1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kai hari a kan masu ciwon Ebola

August 17, 2014

Wasu mutane ɗauke da makamai kirar gargajiya sun kai hari a kan wata cibiya da ake jinyan masu fama da ciwon Ebola a birnin Monrovia na Liberiya.

https://p.dw.com/p/1Cw7j
Ebola West Point Slum Infizierte verlassen Isolierstation
Hoto: John Moore/Getty Images

Wani jami'in na ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya na ƙasar, George Williams ya ce daga cikin marasa lafiya guda 29 da suka karɓa a asibitin na wucin gadi ,17 sun tsere sakamakon hare-haren.

Masu jinyar waɗanda aka tattarasu a cikin wata makarantar waɗanda 'yan uwansu suka kai su da ƙarfi da yaji domin a bincikesu. Ana ba su kulawa ta farko kafin a isar da su a asbiti bayan da aka gano cewar suna ɗauke da cutar ta Ebola. Tun da farko a kwanaki huɗun da suka wuce tara daga cikinsu sun mutu yayin da a ranar Asabar wasu uku suka kwanta dama. Ya zuwa yanzu ba a san dalilan da ya sa maharan waɗanda galibi matasa ne suka kai harin ba a cibiyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu