1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe wani jami'in tsaro a Mali

Gazali Abdou TasawaJune 10, 2015

Mayaƙan 'yan jihadi su kimanin 30 sun ƙaddamar da hari a barikin sojan Misseni na ƙasar Mali inda suka kashe wani jami'in tsaro ɗaya:

https://p.dw.com/p/1FegH
Symbolbild Soldaten Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A ƙasar Mali mayaƙan 'yan jihadi sun bindige wani jami'in tsaro a lokacin wani hari da suka ƙaddamar a yau Laraba a wata cibiyar sojoji dama barikin 'yan sanda da na jami'an garin Misseni na kudanccin ƙasar kusa da kan iyaka da ƙasar Cote D'Ivoire da kuma Burkina Faso.

Wani ɗan majalissar dokokin garin na Misseni ya shaida wa kampanin dillacin labaran Faransa na AFP cewar a tsakiyar dare ne mayaƙan 'yan jihadin su kimanin 30 wasu a mota wasu a babur wasunsu kuma a kas suka ƙaddamar da harin akan barikin sojan garin suna ta kabbara.

Maharan sun karɓe barikin sojan garin na Misseni inda suka kafa tutarsu baƙa.Hukumomin tsaron Malin sun tabbatar da afkuwar wannan hari dama mutuwar jami'in tsaro.