1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun mika kai a Najeriya

July 6, 2017

Rundunar Sojojin Najeriya ta gabatar wa manema labarai mayakan Boko Haram 57 daga cikin 700 da ta ce sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga rundunar Operation Lafiya Dole a Maiduguri.

https://p.dw.com/p/2g49C
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

A farkon makon nan ne rundunar sojojin Najeriya ta ayyana cewa akwai mayakan Boko Haram kimanin 700 da suka amince su ajiye makamansu tare da mika wuya ga gwamnati domin wanzuwar zaman lafiya.

Bisa wannan ne a ranar Laraba da maraice rundinar tabbatar da tsaro ta Operation Lafiya Dole a Maiduguri ta gabatar da wasu mutane 57 da ta ce su mayakan Boko Haram da suka yarda su mika wuya ga gwamnatin Najeriya daga cikin wadancen 700.

Nigeria Soldaten in Damboa
Dakarun yaki da Boko Haram a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Kwamandan rundunar ta Operation Lafiya Dole Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ce wadannan mayakan Boko Haram kashi na farko ne da suka ajiye makamai domin kashin kansu domin rungumar zaman lafiya inda nan gaba sauran za su mika kansu su ma.

To sai dai kwamandan bai fayyace yadda aka yi yarjejeniyar ajiye makaman ba da kuma irin ka'idoji da aka gindaya kafin amincewar mayakan su mika wuya ga sojojin Najeriya. A jawabai da suka yi a madadin sauran biyu daga cikin mayakan Boko Haram da suka mika wuya wanda Sojojin ba su yarda su bayyana sunansu ko garuruwansu ba sun ce sun gane abin da suke yi ya sabawa addini kuma sun nemi sauran mayakan da su ajiye makamansu su kuma yi biyayya ga gwamnatin Najeriya.