1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun shiga cikin 'yan gudun hijira

Salissou Boukari
July 2, 2017

Jami'an tsaro a jihar Borno a tarayyar Najeriya sun gano mayakan Boko Haram daga cikin 'yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Kamaru, a cewar wani jami'in cibiyar agaji ta jihar Borno.

https://p.dw.com/p/2fmZl
Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Wraren tantance 'yan gudun jihira a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/EPA/Stringer

An kama 'yan Boko Haram guda 09 da kuma masu mara musu baya guda 100 daga cikin 'yan gudun hijira 920 yayin wani bincike da jami'an tsaro suka aiwatar cikin 'yan gudun hijiran da suka dawo daga birnin Banki da ke kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Tun farkon wannan shekara dai, mayakan na Boko Haram na kai hare-hare ga sojojin Najeriya, da kuma kashe fararan hula da dama ta hanyar kai hare-haren kunar bakin wake, sannan kuma tun daga watan Yuni da ya gabata, mayakan na neman sake dawo da hare-haren na su ya zuwa birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno.

Rikicin Boko Haram a arewacin Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20.000, tare kuma da tilasta wa wasu miliyan 02 da dubu 600 barin gidajensu a matsayin 'yan gudun hijira.