1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na riguntsminin zuwa Jamus

Pinado Abdu WabaSeptember 3, 2015

Sun yi ta damben shiga wani jirgin da suka zaci ya fito yammacin Turai ne ashe ba nan ya nufa ba, dan haka suka bijirewa matakin zuwa sansanin da aka tanadar musu.

https://p.dw.com/p/1GQqx
Ungarn Flüchtlinge am Bahnhof Keleti Budapest
Hoto: Reuters/L. Balogh

An sami wani yanayi mai muni a kasar Hungary lokacin da 'yan gudun hijira suka yi dambe da turereniya dan darewa wani jirgin da suka zaci cewa ya doshi yankin yammacin Turai ne. Tunda sun dade ba su ga jirgin da ya fito yankin ba

Sai dai jirgin na barin tashar da ya dauke su, suka gano cewa 'yan sandan Hungary sun yi musu zamba cikin amince ne, domin sun dakatar da jirgin suka fara kokarin kai su wani sansanin 'yan gudun hijira. 'Yan sandan sun yanke wannan shawarar ne bayan da suka sake bude tashar jirgin Keleti wanda suka kulle na tsawon kwanaki biyu a dalilin 'yan gudun hijirar.

'Yan gudun hijirar dai sun yi ta nuna turjiya, wani mutumi ma janyo wata mata ya yi da danta ya jefa su a kan layin dogon ya kuma ki ya tashi har sai da wasu manyan 'yan sanda suka ciccibesu daga wurin. kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce da yawa daga cikin 'yan gudn hijiran kin sauka suka yi daga jirgin domin su shiga motocin bus bus din da aka yi musu tanadi domin karasawa da su can sansanonin da aka yi musu tanadi.