1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun ja hankali a Malta

Yusuf Bala Nayaya
June 14, 2019

Shugabanni daga kasashen kudancin Turai sun taru a Malta a fafutukarsu ta yin baki guda kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da siyasa gabanin tattaunawar hukumar zartarwar Tarayyar Turai a mako mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3KUeC
Migranten vor der libyschen Küste
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Heinz

Manyan batutuwa da suka ja hankali a taron na Valleta babban birnin Malta sun hadar da batun samar da aikin yi da batun 'yan gudun hijira da sauyin yanayi. Taron dai ya samu halartar shugabanni daga Faransa da Italiya da Spain da Portugal da Girka da Cyprus da Malta.

Yayin da Spain ke fafutuka ta daga martabarta cikin shugabanci na EU da kuma son ganin EU ta kara inganta dangantakarta da Maroko babban batun dai na zama kokari na hana shigowar bakin haure daga Afirka zuwa Turai. Italiya da Malta na son ganin an tsaurara ga batun ba da mafakar siyasa da tsare-tsaren da suka shafi bakin 'yan gudun hijira. Ga Faransa kuwa batun sauyin yanayi shi ne babban abun da ke gabanta.