1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijra sun yi yawa a Turkiyya

Mahmud Yaya AzareSeptember 23, 2014

Mahukuntan Turkiyya na kwatanta kwararar 'yan gudun hijira a kasarsu da annoba, sun ce abin tausayi ne yadda mata da kananan yara ke kwana da kwanaki ba abin kaiwa bakin salati

https://p.dw.com/p/1DJKY
Grenze Syrien Türkei Flüchtlinge 22.9.2014
Hoto: Reuters/Murad Sezer

Dubu dubatan 'yan gudun hijirar Siriya, wadanda samamen da kungiyar IS ke kaiwa garuruwansu ya tilasta musu ficewa daga cikinsu, na cikin mawuyacin hali a sansanonin wucin gadin da aka jibgesu a kasar Turkiya.

Kamar yadda mahukuntan Turkiya suka ba da sanarwa, wannan shi ne adadi mafi yawa na 'yan gudun hijirar da suka shiga kasar a tashi daya, yadda ta kimanta adadinsu da dubu 130, ban da daruruwan da ke ci gaba da yin tururuwa.

Shugaban lura da 'yan gudun hijira na garin Bukamal, da ke kan iyaka, Nauraz Duga, ya siffanta tultular da 'yan gudun hijirar suke yi da annoba

"Tururuwar da mutane ke yi tana da ban tsoro da tausayi. Ba ta yadda za'a bar irin wannan aikin ta'asa ya ci gaba da faruwa. Duk da karar da kasar Turkiya ta jima tana mana, a wannan karon kam za'a kureta. Muna kira da ayi gaggawar tsaftace mana yankinmu daga wadannan miyagu, don mutanenmu su koma gidajensu."

Halin da kananan yara ke ciki abin tausayi ne

Wata tsohuwa da ke wannan sansani na Bukamal, ta nuna takaicinta da mawuyacin halin da suka shiga ita da jikokinta

"Mene ne laifin wadannan yara kanana da za su kwana biyu basu dandana ko loma ba? Haka muka fito, sa kayan jikinmu, domin idan ana ta kai ba'a ta kaya. Ba dai abin da za mu ce, sai Allah ya isa."

Tun bayan fara yakin basasa a kasar Siriya shekaru kusan hudun da suka gabata dai, 'yan gudun hijirar Siriya kusan dubu dari biyu ne ke samun mafaka a kasar ta Turkiya, wadanda kuma ke zaune cikin yanayin ba yabo ba fallasa, idan aka kwatantasu da takwarorinsu da ke wasu kasashen makwabta, lamarin da ya ke matukar tasiri a tattalin arzikin kasar, musamman bisa la'akari da yadda alkawuran da kasashen da ke kiran kansu kawayen Siriya suka yi na tara gidauniyar lura da 'yan gudin hijra ya zama maganar fatar baki.