1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan italiya da aka sace sun koma gida

Ahmed SalisuJanuary 16, 2015

Matan nan 'yan Italiya da aka sace a Siriya lokacin da suke aikin agaji sun isa gida, kwana guda bayan da wadanda ke tsare da sun sake su.

https://p.dw.com/p/1ELSo
Italien Zwei in Syrien freigelassene Geiseln wieder in Rom
Hoto: Reuters/A. Bianchi

Ministan harkokin wajen Italiya din Paolo Gentiloni da wasu mukarraban gwamnati ne suka marabci Greta Ramelli da takwararta Vanessa Marzullo a wani filin jirgin sama na sojin da ke kusa birnin Rome da sanyin safiyar wannan Juma'ar

Masu aiko da rahotanni suka ce saukarsu ke da wuya aka wuce da su asibiti don duba lafiyar inda daga bisani za su gana da masu gabatar da kara na kasar kan harkokin da suka danganci yaki da ta'addanci.

A karshen watan Yulin shekarar da ta gabata ne dai aka sace wadannan mata a birnin Aleppo na kasar Siriya kwanaki uku kacal bayan isarsu kasar daga kasar Turkiyya da ke makotaka da Siriyan.