1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jihadi sun dauki alhakin hari a Mali

Salissou BoukariAugust 11, 2015

Daya daga cikin jagororin 'yan jihadin arewacin kasar Mali kuma tsohon mayaki a kungiyar Mokhtar Belmokhtar Souleyman Mohamed Kennen ya dauki alhakin harin da aka kai a Sevare

https://p.dw.com/p/1GD4d
Hoto: Getty Images/AFP

Shi dai wanda ya dauki ahakin kai harin na hotel din na birnin Sevare Souleyman Mohamed Kennen na a matsayin na kusa da Malamin nan mai tsatsauran ra'ayin adini Amadou Koufa, kuma tsohon mayakin a cikin kungiyar Mokhtar Belmokhtar na kasar Algeriya inda ya ce harin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 15, alhali adadin da hukumomin kasar suka bayar ya ce mutun 13 ne suka rasu.

Da yake bayani wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, Souleyman Mohamed Kennen ya ce Allah ya kai 'yan jihadi a Sevare zuwa ga makiyan Muslunci, kuma ya ce sun kashe kafirai da masu hada baki da su. Inda ya ce mayakansu ne kuma suka hallaka sojojin kasar Mali guda uku tare da jikkata wasu sojojin hudu a yammacin jiya Litinin. sannan ya kara da cewa kuma Cheik Amadou Koufa ya yi musu addu'o'in cin nasara ga wannan hari.