1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar Amirka sun soke Obamacare

Mouhamadou Awal Balarabe
May 5, 2017

Majalisar wakilan Amirka ta amince da kudirin soke shirin inshorar kiyon lafiya da shugaba Obama ya samar a 2010, lamarin da ke zama nasarar farko ga sauye-sauyen da Donald Trump ya sa a gaba.

https://p.dw.com/p/2cPY0
USA Abstimmung über Obamacare in Washington
Hoto: Reuters/U.S. House TV

Majalisar dokokin Amirka ta soke tsarin kiwon lafiya na Obamacare da gwamnatin da ta shude ta samar, bayan da 'yan majlisa 217 daga cikin 430 suka kada kuri'ar amincewa da manufar. Wannan dai ita ce nasara ta farko da shugaba Donald Trump ya samu na manufofin da yake son aiwatarwa, tun bayan da ya dare kan kujerar mulkin Amirka kwanaki fiye da 100 ke nan da suka gabata.

 Idan za a iya tunawa dai gwamnatin Trump ta janye kudirin farko da ta mika wa majalisar dokki a ranar 24 ga watan Maris da ya gabata, sakamakon rashin samun jituwa tsakanin 'yan majalisar ta Republican masu rinjaye kan tsarin na kiwon lafiya, duk  da matsin lamba da suka fuskanta.

Shi dai tsohon shugaba Barack Obama ya samar da wannan shiri ne a shekara ta 2010 da zummar bai wa dimbim Amirkawa da ba su da hali damar kula da lafiyarsu yadda ya dace. Sai dai shugaban masu rinjaye na Repablican a majalisar dokokin Paul Ryan, ya ce amincewa da dokar na nuni da cika alkawarin da suka dauka. Sai dai kudirin da bukatar amincewar majalisar dattawa kafin ta zama doka.