1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan matan Chibok da kyamar baki a Afirka ta Kudu

Mohammad Nasiru AwalApril 17, 2015

Jaridun na Jamus sun mayar da hankali kan cika shekara guda da sace 'yan matan Chibok da yawan bakin haure 'yan Afirka da ke shigowa Turai ta tekun Bahar Rum da boren kyamar baki a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1FA0b
Symbolbild Entführungen von Frauen und Mädchen in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

Bari mu fara da sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi game da 'yan matan Chibok.

Ta ce shekara guda ke nan da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 na makarantar sakandare a garin Chibok, har yanzu kuma ba a san makomarsu ba. Shin an yi wa wasu auren dole ne ko kuma an tilasta musu kai harin kunar bakin wake? Wannan dai wata ta'asa ce maras misaltuwa. Kungiyar Amnesty International ta yi kiyasi cewa akalla mata da 'yan mata 4000 Boko Haram ta yi garkuwa da su tun farkon shekarar 2014 sannan yawan wadanda aka kashe ya kai 5500, kuma Chibok daya ne daga cikin munanan ayyukan kungiyar ta Boko Haram, wanda hakan ya nuna karara gazawar gwamnati wajen yaki da ta'addanci.

Kawararar bakin hauren Afirka a Turai

Kasashen kudancin Turai irinsu Italiya da Girka sun rasa yadda za su yi da dubun dubatan 'yan gudun hijira daga Afirka inji jaridar Der Taggesspiegal wadda ta kara da cewa tururuwar bakin haure daga nahiyar Afirka zuwa kasashen Turai ta kai wa gwamnatin kasar Girka iya wuya, inda ta yi barazanar tura su zuwa wasu kasashen tarayyar Turai. Gwamnati a birnin Athens ta zargi kasashen arewacin Turan da ba wa 'yan gudun hijirar kasar Siriya fifiko a kan 'yan Afirka, a saboda haka kasar ke son yin gyara a manufarta da ta shafi 'yan gudun hijira don saukaka wa 'yan Afirka karasawa zuwa kasashen arewacin Turai da suke da sha'awar zuwa. Jaridar ta ce a kwanakin nan an samu karuwar yawan 'yan gudu hijirar Afirka da ke bi ta Libya su hau jiragen ruwa marasa inganci wajen tsallake tekun Bahar Rum zuwa Italiya. Lamarin da ke janyo asarar dubban rayuka.

Italien Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa/Italian Navy Press Office

Boren kyamar baki 'yan Afirka a Afirka ta Kudu

To yayin da a kasar Girka gwamnati ke kokarin kyale 'yan gudun hijirar Afirka su karasa arewacin Turai, a Afirka ta Kudu kuwa boren kyamar baki 'yan kasar ke yi inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a cikin sharhin da ta yi.

Gewalt gegen Einwanderer in Johannesburg
Hoto: picture alliance/dpa/K. Ludbrook

Ta ce sabili da munanan tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kai wa baki 'yan Afirka 'yan ci-rani a Afirka ta Kudu, gwamnatin kasar Malawi ta ba da sanarwar kwashe 'yan kasarta fiye da 400 daga Afirka ta Kudu. 'Yan kasar ta Malawi da sauran baki daga wasu kasashen Afirka sun nemi mafaka a babban filin wasan kwallon kafa da ke wajen birnin Durban, bayan kisan wasu 'yan Afirka akalla mutum biyar ciki har da wani yaro dan shekaru 14 da masu boren kyamar bakin a Afirka ta Kudu suka yi. Jaridar ta ce ana zargin Basaraken Zulu Goodwill Zwelethini da haddasa boren bayan furucin da ya yi da a kori baki daga kasar. Sai dai tuni Basaraken ya karyata wannan zargi yana mai cewa an yi masa mummunar fahimta. Yanzu haka dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta dauki matakan kawo karshen boren kyamar bakin a kasar.