1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan Rasha dubu 25 sun dawo gida

Pinado Abdu WabaNovember 9, 2015

Zun bayan harin da ya afku a karshen watan Oktoba, 'yan yawon bude idon Rashar ke dawowa gida sakamakon fargaba.

https://p.dw.com/p/1H2HU
Ägypten Sharm El-Sheikh Touristen
Hoto: Getty Images/AFP/M. El-Shahed

'Yan yawon bude idon Rasha, su su dubu 25 suka dawo gida daga Masar a karshen makon da ya gabata. Firaministan Rashan Dimitri Medvedev ya baiyana hakan yayin da yake ganawa da 'yan majalisa, inda ya ce a yanzu haka wasu karin mutane dubu 55 suna kasar Masar din har yanzu, suna jira a kwaso su.

Shugaban hukumar kula da yawon bude ido na Rashar ya ce a yanzu haka dai, masu yawon bude idon na cigaba da dawowa gida ba tare da kayayyakinsu ba, kuma jiragen yawo marasa fassinja, na cigaba da zuwa Masar dan dauko su.

Wannan na faruwa ne duk da cewa shugaba Vladimir Putin ya bada umurnin dakatar da tashin jiragen yawo daga Rasha, sakamakon hatsarin da ya afku a karshen watan Oktoba, abin da ake ganin zai iya tasiri a yanayin tattalin arzikin kasar ta Masar.