1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda hudu aka bindige a Amirka

Suleiman BabayoJuly 8, 2016

Zanga-zanga ta shiga rudani lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta kan 'yan sanda a Dallas da ke Amirka, bayan kisan wasu bakaken fata biyu da 'yan sanda suka yi.

https://p.dw.com/p/1JLZU
USA Dallas Schießerei bei Demonstrationen gegen Polizeigewalt
Hoto: Getty Images/AFP/L. Buckman

Hukumomi a Dallas da ke kasar Amirka sun tabbatar da cewa 'yan sanda hudu sun mutu, sannan wasu bakwai suka samu raunika sanadiyar harbi da bindiga, lokacin ake zanga-zanga nuna rashin jin dadi da halaka wasu bakaken fata biyu da jami'an tsaron 'yan sanda suka yi.

Babban jami'in 'yan sanda na Dallas ya shaida wa taron manema labarai cewa 'yan sanda 11 aka harba, kuma daga ciki hudu sun halaka, inda ake neman mutumin da aka yi imanin yana da hannu wajen harbe-harben.

Tun farko Shugaba Barack Obama na kasar ta Amirka ya nuna damuwa bisa tsarin shari'ar da ya gaza shawo kan matsalar.