1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na ci gaba da binciken harin London

March 23, 2017

A dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci-gaba da nuna alhini da goyon baya ga Birtaniya, jami'an tsaro sun duka ka'in da na'in wajen gano gaskiyar lamarin.

https://p.dw.com/p/2ZpNE
London nach dem Attentat - Blumen
Hoto: Getty Images/C. Court

Wanda ya kai harin wanda daman sananne  ne wajen 'yan sanda  tun da farko ya yi  amfani da wata motar wanda ya durfafi  gungun mutane da ita a kan gadar masu tafiya a kasa a Wesminister kafin daga bsanin  ya yi kokarin tsallaka ginin majalisar rike da wuka a hannunsa, wadda yana ckin yin gudun ya caka wani dan sanda,daya daga cikin masu gadin majalisar anda kuma bai kai laari ba,  

Babban kwamman da na 'yan sandar dake yaki da ta'addanci a Birtaniyar Mark Rowley ya ce yanzu haka sun cafke mutane guda bakai wadanda ke da ala da wanda ya kai harin sannan kuma ya bayyana halin da ake ciki

"Alkalluma na karshe da muke da su  sun tabbatar da cewar mtane hudu suka mutu wasu 29 na kwance a asibiti, sai dai bakwai daga cikin wadannan mutanen sun cikin halin mutu kwaikwai rai kwaikwai, amma shi wanda ya kai harin mun hallakashi".

Daga cikin wadanda ke kwance a asibitin suna jinya akwai dalibai uku 'yan kasar Faransa wanda ke yin ziyara a birtaniyar da wasu 'yan yawon shakatawa guda biyar na Koriya ta Kudu, kuma a lokacin da ta ke yin jawabi dazu dazunnan firaminstar Birtaniyar Theresa May ta bayyana takaicinta a game da abinda ya faru.

Theresa May Premierministerin England
Fraiministan Birtaniya Theresa MayHoto: Reuters/Parliament TV

"Matsayin barazanar taadancin da Birtaniya ke fuskanta ta tabbata, duk kuwa da cewar an kwashi dogon lokaci,ba kaimana hari ba ,sai dai duk da irin wannan barazana da muke fuskanta da ta kai kololuwa bamu da fargaba zamu ci gaba da yakar ta'addanci hasali ma wannan hari zamu nemi masu hannu a ciki".

Wannan hari dai shi ne irinsa mafi muni da aka kai a Birtaniya tun bayan na bakwai ga watan Yuli na shekara ta 2005 wanda kungiyar Alqaida ta kai wanda a ciki mutane 56 suka mutu, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya isar da taaziyarsa ga gwanatin birtaniya sannan kuma ya kara da cewar:

"Abin da ya kamata mu gane shi ne cewar ta'addanci abu ne da ya shafemu gaba daya, Faransa wacce ita ma ta fuskanci hare haren na taddanci a yau mu san irin abinda al ummar birtaniya ke ji na radadi, ya ce dole mu mayar da martani a kan wadannan hare hare."

London Tag danach
Jami'in tsaro a kan aikiHoto: Getty Images/AFP/J. Tallis

Shi kuwa firaminintas Japan Shinzo Abbe cewa ya yi, ya zama wajibi a hada karfi da karfe domin yakar ta'addanci a duniya.

"Japan za ta hada karfi da birtaniya domin dakile taaddanci wanda ke zaman babbar barazana ga duniya, ba zamu yi kasa a gwiwa ba".

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi Allah wadai da Lamari yayin da kasashen China da Denmark da Rasha da Beljium, da kuma wasu karin kasashen da dama suka yi Allah wadai da harin.