1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun yi kisa a Kwango

January 21, 2018

'Yan sanda a Kwango sun halaka rayuka tare da jikkata wasu masu yawa a zanga-zangar da aka gudanar ta adawa da Shugaban kasar mai ci. A karshen watan Disambar bara ma dai 'yan sandan sun kashe wasu mutanen a kasar.

https://p.dw.com/p/2rFjf
Proteste im Kongo
Hoto: Reuters/K. Katombe

Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan sanda a Kinshasha sun kashe muatne akalla biyar tare da jikkata wasu a arangamar da suka yi da masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.

Wasu Kiristoci mabiya darikar Katholika da ma wasu masu fafutuka ne dai suka gudanar da zanga-zangar ta yau, inda rahotanni suka ce akalla rayuka biyar.

Biranen Kinshasha da Goma da Lubumbashi, na daga cikin manyan garuruwan kasar da mutanen suka mamaye.

A ranar 31 ga watan Disambar bara ma dai 'yan sandan kasar suka kashe mutane bakwai lokacin da suke nuna bukatar shugaba Kabilan ya sauka daga mulki, shugaban da wa'adinsa ya cika tun cikin sheakarar 2016.