1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya sun ja damarar farautar 'yan Shi'a

July 30, 2019

'Yan sanda a Najeriya, sun bukaci jama'ar kasar da su taimaka masu a wani sabon shirinsu na kama 'ya'yan kungiyar Shi'ar nan ta malam Ibrahim el-Zakzaky.

https://p.dw.com/p/3N1R1
Nigeria Anschlag ARCHIVBILD 19.05.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Rundunar jami'an 'yan sanda a Najeriya, ta bukaci jama'ar kasar da su taimaka mata a wani sabon yunkurinta na kama 'ya'yan kungiyar Shi'ar nan ta malam Ibrahim el-Zakzaky a fadin kasar, kungiyar da hukumomin Najeriyar suka haramta ta a yanzu.

Haramta kungiyar Islamic Movemnet of Nigeria dai ya biyo wata zanga-zangar mako guda da ta kaure tsakaninta da jami'an 'yan sandan.

Shugaban 'yan sandan kasar Mohammed Adamu, yayin wani jawabin da ya yi wa manyan jami'an rundunar a yau, ya ce sun bude kofofin karbar bayanai daga 'yan Najeriya don gano duk inda 'ya'yan kungiyar manyansu da kananansu suke a kasar don hukunta su.

Shugaban 'yan sandan ya ce daga yanzu, ana daukar duk wani dan kungiyar karkashin malam el-Zakzaky a matsayin dan ta'adda, kuma haramun ne su gudanar da duk wani tattaki a Najeriyar.