1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya sun kame wasu 'yan jarida

April 9, 2013

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewar rundunar 'yan sanda kasar ta damke wasu manema labarai hudu wanda ke yi wa jarida Leadership aiki.

https://p.dw.com/p/18C7O
People read local newspapers with the headline 'We've killed 7 foreign hostages' on a street in Kano, Nigeria, Sunday, March. 10, 2013. The United Kingdom's military says its warplanes recently spotted in Nigeria's capital city were there to move soldiers to aid the French intervention in Mali, not to rescue kidnapped foreign hostages. The Ministry of Defense said Sunday that the planes had ferried Nigerian troops and equipment to Bamako, Mali. An Islamic extremist group in Nigeria called Ansaru partially blamed the presence of those planes as an excuse for claiming Saturday that it killed seven foreign hostages it had taken. ( AP Photo/Sunday Alamba)
Nigeria Extremistengruppe Ansaru GeiselnahmeHoto: picture alliance/AP Photo

Su dai wadannan 'yan jarida sun shiga hannun 'yansanda ne sakamakon wani labari da su ka buga game da wata takarda da fadar shugaban kasar ta fidda da ke bada umarnin dagulawa 'yan adawa lamura da ma dai rarraba kawuwunansu gabannin zabukan shekara ta 2015.

Fadar shugaban kasar dai ta musanta wannan labarin to sai dai jaridar ta Leadership ta ce babu batun kage ko shaci fadi a cikin labarin da ta buga, hasali ma ta buga kwafin takardar umarnin da fadar shugaban kasar ta bada dangane da wannan batu a wani mataki na nuna sahihancin labarin nata.

Kawo yanzu dai jami'an tsaron na Najeriya na rike da wadannan 'yan jaridu hudu, inda manajan darakatan kamfanin jaridar ta Leadership Azubuike Ishiekwene ya yi kira ga rundunar 'yan sandar kasar da saki ma'aikatan na su.

Tarayyar Najeriya dai kamar dai yadda kungiyoyin kare hakkin 'yan jaridu ciki har da kwamitin kare manema labarai da ke da mazauninsa a birnin Newyork na kasar Amurka su ka shaida na daga cikin kasashen da ake suka wajen tauye 'yancin fadin albarkacin baki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Saddisou Madobi