1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasar Afirka na ajiyar kudadensu a Turai.

Philipp Sandner MNA/ATB
February 21, 2019

Yayin da gwamnatocin Turai ke kara nuna bukatar yaki da cin hanci da rashawa, a lokaci guda sashen shari'a a nahiyar ta Turan na fuskantar kalubale wajen bin diddigin lamura da dama da suka shafi halasta kudin haramun.

https://p.dw.com/p/3DokC
Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel Guterres
Hoto: Palestinian Presidency

Jean-Jaques Lumumba, jika ga shugaban Jamhuriyar demukuradiyar Kwango na farko Patrice Lumumba, ya kasance daraktan sashen kula da ba da bashi na wani bankin kasar Gabon da ke a birnin Kinshasa, rayuwarsa ta sauya cikin dare daya lokacin da ya janyo hankalin shugaban bankin dangane da wata hada-hadar kudi a bankin da ya kasa gane mata. Ya tsere zuwa kasar Faransa, inda ya fito da labarin na kokarin halasta kudin haramu da ya kai Euro miliyan 40 daga tsohon bankinsa.

"Wasu kamfanoni na kurkusa da tsohon shugaban kasa Joseph Kabila na cikin wannan hada-hada. A lokacin wani na hannun damar Kabila ne shugaban bankin. Matsalar da na samu shi ne sukan hada-hadar da na yi. An yi ta mini barazana abin da ya sa na gudu daga kasar shekaru biyu da rabi da suka wuce."

Europa Finanzen l Steuer auf Finanztransaktionen l Europäische Zentralbank Euro-Skulptur
Hoto: Getty Images/AFP/D. Roland

Yanzu dai Lumumba ya kai wannan batun gaban wata kotu a Faransa, amma lauyansa ya ce abin da wuya, sai dai ya yi fatan samun nasara.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kai batun cin hanci da ya shafi shugabannin Afirka a gaba wata kotu a Turai ba. A shekarar 2017 wata kotu a Faransa ta yanke wa Teodorin Obiang, dan tsohon shugaban kasar Equitorial Guinea, hukunci a bayan idonsa na daurin shekaru uku a kurkuku bisa laifin almundahana da kudin kasa da kuma halasta kudin haramun. An kwace kadarorinsa a Faransa ciki har da wani kasaitaccen gida da kudinsa ya kai Euro miliyan 100. A kasar Switzerland ma an yi masa makamanciyar wannan shari'a inda aka yi gwanjo kadarorinsa aka kuma mayarwa kasar da kudaden don gudanar da ayyukan more rayuwa na al'umma. Hukuncin na zama wata nasara ga kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa irinsu Transparency International, sai dai har yanzu da jan aiki a gaba inji Gillian Dell ta TI.

Belgien Treffen Außenminister Afrikanische und Europäische Union in Brüssel
Hoto: Getty Images/AFP/J. Thys

"Babu wani ci-gaba na a zo a gani a wannan fannin. Muna bukatar ganin an samu ci-gaba ba kawai wajen hukunta masu laifi ba, har ma da matakan rigakafin halasta kudin haramun. Tun wasu shekaru muke bukatar da a kara fayyace sunayen masu mallakar asusun banki da ake budewa da sunan bogi."

Ita maSarah Saadoum ta kungiyar HRW ta ce almundahana a kasashen Afirka na barazana ga samar wa al'umma ababan more rayuwa tana mai ba da misali da kasar Equitorial Guinea mai arziki man fetur.

Har yanzu kotuna a Turai na dari-dari kan irin wannan batun, suna tsoron zargin da wasu ke yi na sabon salo na mulki mallaka.