1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasar Masar sun dauki matakin kawo karshen rikici

February 1, 2013

Wakilan manyan jam'iyyun siyasar kasar Masar sun dauki mataki game da tashin hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar.

https://p.dw.com/p/17WBC
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin wani taro da suka yi birnin Alkahira jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ta shugaba Mohammed Mursi da jam'iyyar salafi mai matsanancin ra'ayin mazan jiya a bangare guda da kawancen 'yan adawa a dayan bangaren sun tsai da shawarar fid da wani jawabi na hadingwiwa wanda a cikin suka yi Allah wadai da tashin hankli na kowace iri da hukunta masu ta da zaune tsaye da kuma haramta yin haka ta daukar matakai na addini. Sun kuma yi kira da a rinka bin hanyonin limana, a kuma shiga tattaunawa domin warware duk wani rikici na siyasa. To sai dai duk haka an yi kira da a sake shiga zanga-zangar nuna adawa da shugaba Mursi a yau juma'a. Mutane 60 ne dai suka rasa rayukansu a rikicin siyasar da aka shafe mako guda ana fama da shi a kasar ta Masar.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman