1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kai hari a wani babban Hotel a Mali

Gazali AbdouNovember 20, 2015

Mutane da dama sun rasu a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a Hotel Radisson da ke birnin Bamako inda suka yi garkuwa da mutane a kimanin 170.

https://p.dw.com/p/1H9o8
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan bindiga kimanin 10 ne dauke da bindigogi suka kutsa a cikin wannan Hotel da kimanin karfe bakwai na safiya inda suka yi garkuwa da mutane kusan dari biyu da suka hada da baki 'yan asalin kasashen waje da dai sauran mazauna Hotel din, da ma ma'aikatansa. Hukumomin kasar ta Mali sun yi amfani da karfin soja tare da taimakon wasu sojojin wasu kasashen ketare domin kai hari na neman ceto mutanan da ake garkuwa da su. Kanal Salif Traore shine ministan tsaron cikin gida na kasar ta Mali:

"Ya ce mun tura jami'anmu domin yin kofar raggo a Hotel din na Radisson, a cikin aikin namu mun samun daukin sojojin Faransa dama na rundunar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a mali wato MUNISMA Kuma tun karfe tara mun kaddamar da hari inda muka yi nasarar ceto wasu mutanen. Yanzu haka mun kai su wani kebabben wuri inda likitocin ke kulawa da su, kuma a lokacin da nake yi maku magana akwai jami'an tsaronmu biyu da suka jikkata"

Mali Geiselnahme Hotel in Bamako Befreiung von Geiseln
Hoto: Imago

Daga cikin mutanan da lamarin ya rutsa da su a cikin wannan hotel rahotannin sun tabbatar cewa da akwai 'yan Algeriya bakoye da 'yan kasar Jamus mutun biyu ,'yan Belgiyam mutun hudu 'yan kasar Sin mutun bakoye 'yan Faransa 2, 'yan Spain biyu, da Amirkawa guda shida, 'yan Indiya 20 'yan Turkiyya Bakoye, biyu 'yan kasar Cote d'Ivoir, da dan kasar Rasha daya, dan kasar Kanada daya dan Senegal daya da kuma 'yan kasar ta Mali mutun 45. Daya daga cikin 'yan kasar ta Mali da aka kubutar daga hannun 'yan ta'addan ya yi tsokaci:

Mali Geiselnahme Hotel in Bamako
Hoto: imago/PanoramiC

"Ya ce tun da sanyin safiya ne na ji kamar karan bindiga, amma sai na yi zaton wasan wuta ne ake yi, shi ya sa har sai da na fito domin in tafi dakin cin abinci, a lokacin ne sai na ga hayaki na tashi ko ina, dan haka a guje na koma dakina. zuwa wani lokaci sai ga jami'an tsaro sun zo suka buga mani daki suka fito da ni tare da gungun wasu mazauna Hotel din. Yanzu ba abin da za ni ce sai godiyar Allah da ya sa na fita ba da wani kwarzane."

Rahotanni daga birnin na Bamako dai na cewa an kawo karshen garkuwar da 'yan bindigar suka yi a wannan Hotel na Morisson inda aka yi nasarar kubutar da illahirin mutanen a raye. sannan wata majiyar tsaron kasar ta Mali ta bayyana cewa an tarar da gawarwakin mutane 18 a cikin Hotel din bayan da aka yi nasarar kashe biyu daga cikin maharan a yayin da yanzu haka jami'an tsaro ke ci gaba da farautar sauran da suka boye a wasu dakunan Hotel din wacce jami'an tsaron ke ci gaba da yi mata kawanya.