1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe mutane 26 a Kenya

June 16, 2014

Wasu mutane da ake kyautata zaton cewar 'yan kungiyar al-Shabab na kasar Somaliya ne sun kai hari a birnin Mpeketoni da ke yammacin Kenya inda suka kashe da dama.

https://p.dw.com/p/1CIzj
Mombasa Anschlag auf radikal islamischen Prediger Ibrahim Ismail
Hoto: Getty Images/AFP

Rahotanni daga birnin Mombasa na kasar Kenya, sun ce akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin da wasu gungun mutane akalla 50, dauke da makammai suka kai a yammacin jiya Lahadi har ya zuwa kusan wayewar wannan Litinin din (16.06.2014), a birnin Mpeketoni dake yammacin kasar ta Kenya.

Da yake magana wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP a yau Litinin, mataimakin Shugaban gundumar ta Mpeketoni Benson Maisori, ya ce kawo yanzu dai sun samu tattara gawarwakin mutane akalla 26, inda suka ajiyesu a dakunan ajiyar gawarwaki, kuma suna ci gaba da neman wasu.

Sai dai kuma a wani adadin da jami'an tsaron 'yan sanda suka bayar, sun ce mutane 14 ne suka rasu, wasu kuma fiye da ashirin suka ji rauni, a cewar kakakin 'yan sandar yankin.

Maharan dai da ake dagantawa da 'yan kungiyar al-Shabab na kasar Somaliya, sun jima ana dauki ba dadi da su a wannan birni na Mpeketoni, inda suka yi kaca-kaca da muhimman gine-gine a birni. Sai dai kuma kura ta lafa a wannan Litinin din.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe