1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun tarwatsa kansu a Chadi

Yusuf BalaAugust 26, 2015

Jami'an sojin suka ce 'yan ta'addar sun yi kokari na kutsa kai cikin sansanin sojin na Kaiga Ngouboua a yankin tafkin Chadi.

https://p.dw.com/p/1GLoT
Bürgerkrieg in Darfur, Sudanesische Rebellen im Tschad
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu 'yan ta'adda guda biyu sun tashi bama-baman da ke jikinsu a gaban sansanin sojan kasar Chadi bayan da suka fiskanci tirjiya daga bangaren dakarun soji da ke gadin kofar shiga wani sansani a Chadi ranar Laraban nan.

A cewar majiyar jami'an sojin wadanda ake zargin da yunkurin kai hari a sansanin soji na zama mayaka ne daga kungiyar tsagerun Boko Haram wadanda dakarun sojan kasar ta Chadi da sojojin kawancensu ke fattattaka.

Jami'an sojin suka ce 'yan ta'addar sun yi kokari na kutsa kai cikin sansanin sojin na Kaiga Ngouboua a yankin tafkin Chadi sai dai basu sami nasara ba, hakan ya sa suka tashi bama-baman da ke jikinsu suka halaka.

Birnin N'djamena na kasar Chadi shi zai karbi cibiyar bada umarni ga dakaru 8,700 na kasashe da suka shiga yaki da mayakan na Boko Haram inda shugabannin dakarun zasu fito daga kasashen Najeriya da Chadi da Nijer da Kamaru da jamhuriyar Bene.

A ranar Larabar ce kuma za a saurari shari'ar mutane 10 da ake zargi da alaka da kai hare-hare a kasar ta Chadi a watan Yuni da Yuli da suka gabata.