1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masoya kujerar shugaban kasa kusan 90

Gazali Abdou Tasawa Mamadou Lamine Ba, YB
January 3, 2019

A Senegal cikin 'yan takarar 87 da suka bayyana sha'awar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2019,  30 ne kawai suka ajiye takardun takararsu a gaban kotun tsarin mulki a karshen wa'adin karbar takardun.

https://p.dw.com/p/3AyBk
Senegal Wahlen 2017
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

A watan Satumba wakilan jam'iyyun siyasa ko kuma kawancen jam'iyyu 87 ne suka karbi takardar shiga takarar a gaban hukumar zaben kasar. To amma kuma a karshen wa'adin aje takardun takarar kasa da mutane 25 ne suka ajiye takardun takarar ta su a gaban kotun tsarin mulkin kasar da suka hada da shugaba mai ci Macky Sall da Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade da Khalifa Sall na cikin wadanda suka ajiye takardar takarar ta su. Sai dai Kalidou Balde daya daga cikin tsaffin shugabannin jam'iyyar PDS ta tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade na ganin da wuya Karim Wade ya kai labari a zaben.

Senegal Dakar Wahl
Hoto: picture-alliance/abaca

A zaben 'yan majalisar dokoki na 2017 akwai kananan jam'iyyun da aka kafa daga bisani amma suka taka rawar gani kamar irin su jam'iyyar PUR wacce ta samu kujeru uku a majalisa. To amma Papo Mane wani dan jarida mai sharhi kan harakokin siyasa a kasar ta Senegal na ganin zai wuya a wannan karo tarihi ya maimaita kansa.

A shekara ta 2000 'yan takara takwas ne suka fafata a zaben shugaban kasar ta Senegal, a 2007 'yan takara 15, a zaben 2012 'yan takara 14. A ranar 24 ga watan Fabrairun wannan shekara ne dai ake gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa a kasar ta Senegal wanda ke zama na 11 da kasar ta shirya tun bayan samun 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallakar kasar Faransa a ranar hudu ga watan Aprilun 1960.