1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Tanzaniya sun yaba da kamun ludayin Magufuli

March 18, 2021

'Yan Tanzaniya na nuna alhinin mutuwar shugaba John Magufuli. Gwamnatin kasar ta sanar da cewa shugaban ya mutu a sakamakon wani nau'i na ciwon zuciya. Sai dai madugun adawar kasar ya ce corona ce ta yi ajalin shugaban.

https://p.dw.com/p/3qoFH
Tansania Präsident John Magufuli verstorben
Hoto: AFP

Kusan makonni biyu aka kwashe, ana tafka muhawara a kan lafiyar marigayi Shugaba Magufuli. A cikin wannan lokaci masu jita-jita a majalisun hira sun rinka batun a matsayin babban maudu’in tattaunawa, a yayin da shafukan sada zumunta suka cika da hotunan Magufuli inda 'yan Tanzaniya suka bukaci gwamnatin kasar ta fito ta gaya musu gaskiyar halin da ake ciki.

Sai dai a yanzu Hassan Sayid wani dan kasar ya ce jita-jitar ta zo karshe, inda ya ce: ‘’Muna masu godiya ga Allah domin da farko an ta yawo da hankalinmu , mutane sun ta yada jita-jita, a don haka muka yi shiru da bakinmu domin ba mu san gaskiyar abin da ke faruwa ba, amma yanzu tun da an bayyana a hukumance, mun faula wa Allah al’amarunmu, shi ne mai badawa kuma kuma mai daukewa.’’

Jaridun Tanzaniya sun raja'a kan mutuwar Shugaba Magufuli
Jaridun Tanzaniya sun raja'a kan mutuwar Shugaba MagufuliHoto: AFP/Getty Images

 A shekara ta 2015 aka zabi John Magufuli a matsayin shugaban kasa wa’adi na farko inda jama’ar Tanzaniyar ta zabe shi domin alkawarin yaki da cin hancin da karbar rashawa da ya yi. To amma mutuncin gwamnatinsa ya shiga cikin wani hali bayan da ya fara sanya kafar wando daya da 'yan adawa gami da kungiyoyin fararen hula.

Sai dai duk da haka Innocent Tionoke, wani dan Tanzaniya, ya ce Shugaba Magufuli ya yi mulki nagartacce. Ya ce "Dr John Magufuli ya yi mana abubuwan ci gaba masu yawan da ba zan iya zayyanawa ba. Muna kaunarsa, ba zan iya siffanta irin kaunar da muke masa ba, amma Allah ya fi mu son shi, sabaoda haka muna masa fatan samun tsira.‘‘

Sanarwar gwamnatin kasar ta ranar Laraba (17.03.2021) da daddare ta nuna cewa shugaba Magufuli ya mutu a sakamakon wani nau’i na ciwon zuciya. To amma jagoran adawar kasar wanda magufuli ya kayar a zaben shugababn kasar Tanzaniya na watan Oktoban da ya gabata.Tundu Lissu ya ce rufa-rufa ce kawai gwmanati ke yi; coronavirus ce ta yi ajalin shugaban da ya rinka yi mata rikon sakainar kashi, kuma wannan ya nuna cewa mai hali baya barin halinsa, duk da batu ne na mutuwa amma sai gwamnatin Tanzaniya ta shirga abin da ya kira karerayi.

Tansania | Oppositionsführer Tundu Lissu
Madugun adawa Tundu Lissu ya ce corona ce ta kashe Shugaba MagufuliHoto: Eric Boniphace/DW

Sai dai Jina Patrice Tarimo na mai cewa duk abin da 'yan adawa za su fada ba zai sauya kimar da suke kallon marigayi shugaba Magufuli ba. Ya ce  "Na fara ganin kokarinsa tun lokacin da yake ministan ayyuka har ya zamo shugabana kasa, shugaba ne da ya yi aiki tukuru, a tsarinsa koda a yanzu kun samu sabanin ra’ayi da shi nan gaba sai an wayi gari kun dawo kun fahimci juna, ina masa godiya, ya yi aiki nagari.‘‘

A bisa tsarin mulkin Tanzaniya, mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu Hassan ce za ta maye gurbin Shugaba Magufuli, kuma za ta ja ragamar kasar har zuwa shekara ta 2025 lokacin da za a gudanar da sabon zabe.